1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Gaza

Abdullahi Tanko BalaJanuary 5, 2009

Halin da ake ciki a cigaba da Kutsawan Dakarun Izraela Zirin Gaza

https://p.dw.com/p/GSKu

Sojojin Israila na cigaba da ruwan bama bamai ba ƙaƙƙautawa a yankin zirin Gaza. A tsawon daren jiya zuwa wayewar gari, dakarun Hamas sun yi ta ɗauki ba daɗi da sojojin Israila a yankin Khan Yunus dake kudancin Gaza. A ɓangare guda kuma kafofin yaɗa labaran Israila sun ruwaito cewa mayaƙan saman Israila sun kai hari da jiragen sama har sau Talatin a wannan yanki.

Tzipi Livni Außenministerin Israel
Tzipi LivniHoto: AP

A dai halin da ake ciki sojojin na Israila na cigaba da kutsawa cikin yankin zirin Gaza tare da rakiyar jirage dake kai farmaki ta sama. Jamián sojin Israilan sun ce a yan saoin da suka wuce sun ragargaza muhimman cibiyoyi dake da nasaba da ƙungiyar Hamas. Maáikatar tsaron Israila ta ce sojojin sun raba Gaza gida biyu bayan karɓe ragamar babbar hanyar da ta raba arewaci da kuma kudancin yankin Falasɗinu. Sun yiwa birnin Gaza baki ɗaya ƙawanya.

Ƙungiyar taimakon jin kai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce Rahotanni sun ce mutane fiye da 500 suka rasa rayukan su a farmakin da Israilan ta ƙaddamar wanda a yau aka shiga kwana goma tana luguden wuta. Jamián Majalisar Ɗinkin Duniya a Gaza suka ce kashi Ashirin cikin Ɗari na mutanen da aka kashe fararen hula ne. Falasdinawa kimanin 13,000 a yankin na Gaza sun rasa gidajen su sakamakon ragargaza gidajen da Israila ta yi inda a yanzu suke zaman gudun hijira.

A yanzu dai kamar yadda gidan talabijin na larabci na Aljazeera ta ruwaito a yau wakilan Hamas gana da shugabannin ƙasar Masar wadda ke kai komo tsakanin Israila da Hamas game da halin da ake ciki a Gaza.

Sai dai yayin da shugabanni da kungiyoyin ƙasa da ƙasa ke kira ga Israila ta kawo karshen wannan taása a waje guda Firaministan Israila Ehud Olmert na tuntuɓar shugabanin domin baiyana musu daáwar Israila na kin amincewa da tsagaita wutan. Olmert ya shaidawa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ya zama wabiji ne ga Israila ta ɗauki wannan mataki kasancewar ba ta da wani zaɓi na dakatar da hare-haren rokokin da Hamas ke yi zuwa cikin Israila. Shima shugaban ƙasar Israilan Shimon Perez yayi bayani da cewa.

Ba zamu amince da wani yanayi Hamas zasu cigaba da harba mana rokoki ba sannan mu tsagaita wuta, wannan sam ma ba abu ne mai maána ba.

A dangane da cigaba da kutsawar da sojojin Israila ke yi a Gaza kuwa Shimon Perez yace ko kadan basu da wata shaáwa ta sake kwance yankin Gaza.

ƙungiyar agaji ta Red Cross tace karuwar jamaá fararen hula da suka jikata a sakamakon wannan farmaki na cigaba da haifar da babban damuwa. Bugu da kari tace babu wutar lantarki a Gaza, asibitoci sun cika da makil da mutane da suka sami raunuka.

Ministan harkokin wajen Israila Tzipi Livni wadda tace bata ga wani halin tagaiyara da ake fuskanta a Gaza ba, ta baiyana farmakin sojin da cewa yana kan hanya.

Gaza Angriff Israel
GazaHoto: AP

"Tace ban fahimci irin yadda ake cewa Israila ta nuna karfi fiye da kima ba, ko da a makon da ya wuce Hamas ta kai hari kan fararen hula a wata makaranta a Israila, saboda haka matakin da muke dauka kawai shine don hana su cigaba da wannan".

A yanzu dai tawagar tarayyar turai ta isa yankin gaban ta tsakiya domin buƙatar kawo ƙarshen yaƙin dake gudana a Gaza. Tawagar na ƙarkashin jagorancin Ministan harkokin wajen jamhuriyar Czech karel Schwarzenberg wanda ƙasarsa ke riƙe da shugabancin karɓa-karɓa na ƙungiyar tarayyar turai. Sauran yan tawagar sun haɗa da Ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner dana Sweden Carl Bildt da kuma kwamishiniyar hulɗa da ƙasashen ƙetare ta ƙungiyar tarayyar turan Benita Ferrero Waldner. Tawagar har ta gana da Ministan harkokin wajen Masar Ahmed Abul Geit a birnin Alƙahira. Yayin da za su nufi Israila da kuma yankin Falasɗinawa dake gabar yamma.

Da yake tsakoci shugaban tawagar kuma Ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner yayi bayani da cewa .

Bernard Kouchner
Bernard KouchnerHoto: AP

"Yace wajibi ne mu yi wani abu, ba batun ikrari ko sukar lamiri, babu kuma zance komawa ga tarihin abin da ya wuce dukkanin mu mun san abin da ya kamata mu yimagana ce ta tabbatar da ƙwaƙƙwarar kudiri na zahiri".