Rikicin Gabas Ta Tsakiya | Labarai | DW | 28.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Gabas Ta Tsakiya

Falasdinawa 7 aka kashe sannan 13 suka samu raunuka a wani farmaki da jiragen saman yakin Isra´ila suka kai kan ´yan takifen kungiyar Jihadin Islami a Zirin Gaza. Jiragen saman yakin isra´ila sun harba makamai masu linzami kan wata mota a sansanin ´yan gudun hijira na Jabaliya, inda suka halaka akalla mutum biyu dukkan su ´ya´yan kungiyar baradan Al-Quds bangaren mayakan kungiyar Jihadin Islami. Wannan farmakin ya zo ne kwana daya bayan da kungiyar ta yi ikirarin hannu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a arewacin Iasra´ila wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum 5 sannan da dama suka raunuka. A halin da ake ciki gwamnatin Isra´ila ta dakatar da duk wata hulda da tuntubar juna da hukumar mulkin Falasdinawa sannan kuma ta ba da sanarwar wani gagarumin shirin kai hare hare a Gabar Yamma da Kogin Jordan.