Rikicin Falasdinawa da Isra′ila | Siyasa | DW | 16.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Falasdinawa da Isra'ila

Duk da matsanancin matakan tsaron da Isra'ila ta dauka a yankunanta dama yankunan Falasdinawa, dubban Falasdinawan sun bazama kan tituna a ranar da suka kira da "Ranar Fushi".

falasdinawa na ci gaba da zanga-zanga

falasdinawa na ci gaba da zanga-zanga

Kama daga Ramallah da Birnin Kudus har zuwa Zirin Gaza, dubun-dubatar Falasdinawan da ke fushi da Isra'ila ne sukai tattaki kan tituna suna rera taken nuna kyama ga abin da suka kira "Cin zali marar iyaka na Isra'ila da kokarin sauya fasalin masallacin Al'Aksa, dangane da wuraren yin ibada a cikinsa da kuma lokotan yin ibadar.

Falasdinawa na nuna fushinsu

Halin da mata da kananan yara kan tsinci kansu a ciki.

Halin da mata da kananan yara kan tsinci kansu a ciki.

Hassan Yusuf kusa a kungiyar Jihadul Islami ya ce yanzu babu wani sauran banbance-banbancen siyasa tsakanin al'ummar Falasdinawa wajen tunkarar shirin da Isra'ila ke aiwatarwa na ganin bayan al'ummarsu inda ya ce zanga zangar da suke yi ta nuna fushinsu ne ga irin halin mamayar da suke fuskanta daga Isra'ila wanda ya zamo wajibi su nuna mata ba fa ita kadai ce a duniya ba.

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas

Goyon bayan gwagwarmayar lumana

Shima kansa shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, wanda wasu ke zargin sa da mika wa Isra'ilan wuya bori ya hau, ya ce shima yana goyan bayan gwagwarmar lumanan da al'ummar Falalsdinawa ke yi don kwato hakkinsu. Ya kara da cewa za su ci gaba da yin gwagwarmaya ta hanyar tattaki a kan tituna kamar yadda za su ci gaba da yi a zaurukan Majalisar Dinkin Duniya da tarukan kasa da kasa har sai sunga bayan abin da ya kira da mulkin mallaka daya tilo mafi tsayi da ya rage a doran kasa.

Sauti da bidiyo akan labarin