Rikicin Boko Haram na ci gaba da daukar hankali | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 27.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Rikicin Boko Haram na ci gaba da daukar hankali

A wannan makon da yawa daga cikin jaridun na Jamus sun yi tsokaci game da tashe-tashen hankula masu nasaba da ayyukan Boko Haram a Najeriya.

A labarinta mai taken farmaki a kan Boko Haram jaridar die Tageszeitung cewa ta yi: Rundunar sojin Najeriya ta fara samun galaba a kan mayakan Boko Haram. Bayan da sojojin suka sake kwace wasu garuruwa masu muhimmanci kamar Baga da ke kusa da tafkin Chadi, yanzu ana kai hare-hare a maboyar masu ta da kayar bayan da ke dajin Sambisa da tsaununkan kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru. Wannan nasarar da sojojin ke samu na yin tasiri a yakin neman zaben da ke tafe. Saboda haka dan takarar neman shugabancin Najeriya karkashin inuwar APC Muhammad Buhari ya jawo hankali cewa gwamnati na son ta yi amfani wannan halin don cimma wasu muradu nata. Jaridar ta ce sai dai har yanzu ana ci gaba da fuskantar tarzomar ‘yan bindigar inda a wannan makon mutane da dama suka mutu a hare-haren kunar bakin wake da kungiyar ta Boko Haram ta kai a wasu sassan arewacin Najeriya.

Sanya 'yan mata kai harin kunar bakin wake

A labarin da ta buga game da rikicin na Boko Haram jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa Boko Haram na tura mata musamman yara suna kai harin kunar bakin wake, kuma wannan rashin imani ne babba.

Boko Haram Nigeria 14.2. Kwadon

Hare-haren Boko Haram sun yi kamari

Ta ce ‘yan matan masu shekaru goma-sha wasu ma kasa da shekaru 10 Boko Haram ke sa su tarwatsa kansu da bama-bamai a cikin jama'a. Kamar a kullum ba safai ake gane asalin wadannan ‘yan matan masu kai harin kunar bakin wake ba, amma jita-jitar da ke yaduwa ita ce wasu daga cikin yara ‘yan matan masu wadanda Boko Haram ta yi garkuwa da su ne kuma ta cusa musu wani ra'ayi daban yayin da wasu majiyoyin kuma ke cewa manyan matan mayakan Boko Haram ne da aka kashe a filin daga.

An taka wa gwamnatin Kenya biriki

Nakasu ga gwamnati inji jaridar Die Tageszeitung lokacin da take tsokaci ga dokar yaki da ta'addanci a Kenya da bisa matsin lamba ‘yan adawa ake yi wa kwaskwarima.

Nairobi Kenia Abgeordnete Parlament Debatte Sicherheitsgesetz 18.12.2014

Karfafa yaki da ta'addanci a kasar Kenya

Ta ce kotun kare kundin tsarin mulkin Kenya ta yi watsi da wasu sassa biyu na dokar yaki da ta'addancin dokar da an amince da ita kamar yadda take da watakila ta takaita aikin ‘yan jarida da rage yawan ‘yan gudun hijira da ke shiga kasar ta Kenya. Kotun ta yanke hukuncin cewa takaita ‘yancin yada labaru da rage yawan ‘yan gudun hijira ya saba wa kundin tsarin mulki. Jaridar ta ce ‘yan adawa da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi nasarar kawo nakasu ga wannan doka da ake takaddama kanta. To sai dai duk da gyara ga wasu sassan dokar, 'yan adawar sun ce za su sake daukaka kara da nufin soke karin sassa na dokar. Su kuma lauyoyin gwamnati a nasu bangaren suna nazarin hukuncin kotun da zumar shigar da kara. Ko da yake wannan wani koma-baya ne ga gwamnatin Shugaba Uhuru Kenyatta amma wasu bangarori na dokar za su yi aiki wato kamar tsare wadanda ake zargi da ta'addanci tsawon kwanaki 360 ba tare da gurfanar da su ba.