1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Najeriya na daukar sabon salo

Usman ShehuNovember 28, 2013

Dubban magoya baya da shugabanin jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya, sun gudanar da zanga-zanga zuwa ofishin hukaumar zaben kasar, duk kuwa da 'yan sanda da tankokin yaki da aka girke.

https://p.dw.com/p/1AQGb
Auf dem Bild: Menschen Protestieren in Abuja, Nigeria gegen Wahlfälschung. Foto: Uwais Abubakar Idris / DW am 28.11.2013.
Wahl Nigeria ProtesteHoto: DW/U.Abubakar Idris

'Ya'yan jamiyyar adawar ta APC a Tarayyar Najeriya, sun rinka rera wake-wake a lokacin da suka yi zanga-zangar lumana da ta sanya harkoki tsayawa cak, a titunan da suka tashi daga helkwatar jam'iyyar zuwa ofishin hukumar zaben kasar. Zanga-zangar da suka yi domin nuna bacin ransu ga yadda hukumar zaben ta gudanar da zabubbuka a wasu jihohin kasar, musamman ma dai Jihar Anambra, ta nuna irin gagarumin goyon bayan da suke da shi. Injiniya Buba Galadima jigo a jam'iyyar ya ce akwai muhimmin sako da suke da shi zuwa ga mahukuntan Najeriyar.

Attahiru Jega, Independent National Electoral Commission Chairman, reads the results sheet before he declared Nigeria's incumbent President Goodluck Jonathan as the winner of last Saturday's presidential election, in Abuja, Nigeria, Monday, April 18, 2011. Jonathan clinched the oil-rich country's presidential election Monday, as rioting by opposition protesters in the Muslim north highlighted the religious and ethnic differences still dividing Africa's most populous nation. (AP Photo/Sunday Alamba)
Attahiru Jega, shugaban hukumar INECHoto: AP

Ya ce "A Najeriya fa ba zabe ake yi ba, ana karfa-karfa ne a rubuta kuri'u ba tare da mutane sun jefa ba. Gwamnati ta yi iya duk abin da za ta iya yi domin ta hana wannan zanga-zangar, muna gwadawa duniya cewa akwai shugabanin da za su iya sadaukar da kansu domin su tabbatar da bin hakkin talaka, koda wannan abin zai ci rayuwarmu kunga an fito da tankunan yaki amma wannan ba zai sa mu sauya abinda muka sanya a gaba ba".

Auf dem Bild: Menschen Protestieren in Abuja, Nigeria gegen Wahlfälschung. Foto: Uwais Abubakar Idris / DW am 28.11.2013.
'Yan sanda da aka turawa masu zanga-zangaHoto: DW/U.Abubakar Idris

An dai sha artabu tsakanin masu zanga-zangar da 'yan sanda da suka girke tankokin yaki a dab da isa ofishin hukumar zaben, inda duk da amfani da karfi da aka yi motar da ke dauke da manyan jam'iyyar da suka hada da Janar Mohammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu bata kaiga isa kofar hukumar zaben ba.

Abin da ya dauki hankali shi ne yadda mata 'yan boko suka shiga wannan zanga-zangar irin su Hannatu Musawa da ta ce babu wata hujja da za a hana su yin zanga-zangar kuma wannan ya nuna a fili irin shirin da suke da shi.

Titel: Parlamentswahl 2011 in Kano State, Nigeria Schlagworte: Nigeria Kano Wahl Wahurne INEC Wer hat das Bild gemacht?: Thomas Mösch Wann wurde das Bild gemacht?: 9.4.2011 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Sarbi, Kano State / Nigeria Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Parlamentswahl am 9.4.2011 im Dorf Sarbi, Kano State. Wahlurne.
Hoto: DW

Ta ce " 'Yancinmu ne mu fito domin abin da muka gani yanzu na rashin gaskiya a wajen zabe, domin lokaci ya zo wanda dole ‘yan Najeriya za su tashi su kwaci 'yancinsu, domin su sani cewa yadda ake sace kuru'un jama'a fa ba zai yiwu ba"

Duk jawabin da ya sosa ran 'ya'yan jamiyyar da shugaban na APC Bisi Akande ya yi a inda jami'an tsaron suka yi dafifi, babu wani jami'in hukumar zabe da ya yi jawabi a kan takardar da suka gabatar.

Zanga-zangar dai na nuna kama hanyar yin fito na fito a tsakanin jamiyyun adawar Najeriyar, da hukumar zaben kasar musamman saboda karuwar korafe-korafe ga yadda ake samun tabarbarewar gudanar da zabubbuka a Najeriyar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Usman Shehu Usman/ MAB