Rikicin ƙasar Mali | Labarai | DW | 02.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin ƙasar Mali

Mali da Niger sun baiyana fargaban su akan jan ƙafa da ƙasashen duniya suke yi wajan ba da haɗin kai ga ɗaukar matakin soji akan 'yan tawayen Mali

Shugabannin ƙasashen Nijar da Mali sun baiyana takaicin su dangane da ja da baya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi akan matakin da ƙasashen suke jiran a ɗauka akan yan tawayen da suka mammaye yankin arewacin Mali kusan watanni tara.

Shugaban gwamnatin wucin gadin na Mali wanda yanzu haka ya ke yin ziyara aiki a Nijar ;da shi da Takwaransa Mahamadou Issoufou sun yi nadama a game da yadda ƙasashen duniyar ke jan kafa wajan ba da haɗin kai ga ɗaukar mataki soji akan yan tawayen na Mali.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasir Awal