Rikici ya sa a dage zabe a Pool na Kwango | Labarai | DW | 16.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici ya sa a dage zabe a Pool na Kwango

A daidai lokacin da 'yan Kwango ke gudanar da tagayen zabuka na majalisar dokoki da kananan hukumomi, gwamnati ta dage zabe a wasu mazabu na Pool sakamakon rikicin da ake fama da shi a yankin.

'Yan Kwango Brazaville fiye da miliyan biyu da suka yi rejista sun fara kada kuri'a da nufin sabunta kujerun 'yan majalisa da kansaloli da kuma shugabannin kananan hukumomi. Jam'iyyar PCT da ke mulki ta tsayar da 'yan takara a mazabu 128 daga cikin 151 da ake da su, yayin da babbar jam'iyyar adawa ta UPADS ta tsayar da 'yan takara 43 a zaben 'yan majalisa. Sai dai kuma gamayar jam'iyyun adawa ta IDC ta ki shiga tagawayen zabukan sakamakon rikicin yankin Pool da kuma kama wasu mambobinsu da aka yi. Turawan zabe dubu uku da 300 ne aka barbaza a sassan Kwango Brazaville da ya saba fuskantar rikici a lokacin zabe.

Hukumomin na Kwango Brazaville sun dage zabe a yankin Pool saboda tashin hankali da ake fama da shi, lamarin da ya kai dubban mutane kaurace wa matsugunansu. Wannan mataki ya shafi mazabu 8 daga cikin 14 da yankin ya kunsa.  A zaben shekarar da ta gabata ma, an yi fama da tashin hankali bayan da shugaban Denis Sassou Nguesso ya yi tazarce bayan da ya kwaskware kundin tsarin mulkin kasar.