1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya kunno kai tsakanin Amirka da China

August 3, 2022

Sabon rikicin diflomasiyya ya kunno kai a tsakanin Amirka da China a kan ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka ke yi a tsibirin Taiwan da China ke ikirarin mallakinta ne.

https://p.dw.com/p/4F4Mx
Taiwan Taipei | Pressekonferenz: Nancy Peolosi und Tsai Ing-wen
Hoto: TAIWAN PRESIDENTIAL OFFICE/REUTERS

Ziyara ce dai ta kyautata alaka da zumunci in ji kakakin majalisar wakilan Amirkan Nancy Pelosi, to amma kuma ta fara rikidewa tana hankoron haddasa tankiya mai yiwuwar haddasa tashin hankali. Tuni dai matakin ya fusata hukumomin China, wadanda suka kaddamar da wani atisayen sojoji na musamman a kusa da Taiwan bayan gargadin da suka yi na cewa idan har 'yar siyasar ta Amirka ta ziyarci Taiwan za ta iya kai wa tsuburin farmaki na soji. Ma'aikatar tsaron Taiwan kuma ta siffanta atisayen da Beijing ta fara yi a matsayin cin fuska ga martabarta ta zama 'yantattar kasa. Shugabar Taiwan Tsai Ing-wen ta kara jaddada matsayarsu kan lamarin tare da yi wa China shagube.

''Duk da yadda muke fuskantar barazanar soji, Taiwan, ba za ta bayar da kai bori ya hau ba. Za mu tashi haikan domibn kare martabar kasarmu da kare mulkin dimukuradiyya. A kan haka ne ma, muke nuna sha'awar aiki hannu da hannu da gwamnatocin dimukuradiyya na dunyia domin tsrae darajar tamu dimukuradiyyar.''

Taiwan Nancy Pelosi und Präsidentin Tsai Ing-wen
Hoto: Taiwan Pool via REUTERS

Hukumomin Taiwan dai na fargabar kada China ta dauki darasi daga abokiyar dasawarta Rasha, a yi musu mamaya irin ta Ukraine. Mahukuntan na Teipei suka ce hakan na nuna irin barazanar da kasarsu ke fuskanta daga China, suna masu tsoratarwa kan cewa idan har China ta yi musu mamaya makamanciyar ta Ukraine, to gaba daya yankin kasashen Indo Pacific za su ji radadin hakan.

To sai dai kuma a wani abu da ke zama tamkar na tare wa aboki fada, Rasha ta yi sauri ta amsa hukumomin Taiwan, inda ministan harkokin wajen Rashar Sergey Lavrov ya yi magana, yana zargin Amurka da tura Nancy Pelosi Ukraine a wani mataki na sharar fagen irin ingiza mai kantun ruwan da Amurkan ta yi wa Ukraine.

Äthiopien | Außenminister Sergei Lavrov
Hoto: Russian Foreign Ministry/TASS/dpa/picture alliance

Duk da cewa Amirka ba ta da yarjejeniyar jakadanci ta kut da kut da Taiwan, Pelosi ta ce babban sakon da ziyararta ke isar wa duniya shi ne Amirka ba za ta yi watsi da tsiburin ba komai wuya komai runtsi. Ta ce hukumomin Washington na farin cikin bunkasa salon dimukuradiyyar Taiwan, wanda ya kai ga zabar mace a matsayin shugabar kasa.

To sai dai duk cewa Pelosin ta kawar da zargin wata markakashiya a ziyarar tata, hukumomin China sun tunasar da Amirka alkawarin da ta dauka a shekara ta 1979, cewa ba za ta yi duk wani abu da zai taba kimar China da mutanenta ba, inda jakadan China a Birtaniya Zheng Zeguang ya ce ziyarar ta Pelosi a tsibirin Taiwan wanda China ke da yakinin mallakinsa amma ya fandare, ta yi hannun riga da yarjejeniyarsu da Amurka, kuma a cewar Chinan ba za ta taba amincewa da saba alkawari irin wannan ba.