1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya haddasa asarar rayuka a Benue

Abdullahi Maidawa Kurgwi
March 7, 2018

A kalla mutane 26 ne aka tabbatar da mutuwar su yayin wasu sabbin hare haren da wasu mahara suka kaddamar kan al'ummomin Omutu dake karamar hukumar Okpokwu da ke cikin jihar Benue.

https://p.dw.com/p/2trfk
Nigeria - Boko Haram Konflikt
Hoto: picture alliance/dpa

Wannan rikici dai a cewar wasu mazauna kauyen na Omutu, ya auku ne bayan wani taron zaman lafiya da ya kankama tsakanin shugabanin Fulani tare da na al'umar Idoma wadanda suke zama tare shekaru da dama.

 

Wasu mazauna yankin sun sheda min cewar harin ya yi kamar na ramakon gayya ne tsakanin Fulani da 'yan kabilar Idoma wadanda aka ce sun kashe wasu Fulani farkon wannan mako, kafin Fulanin suka kai harin ramakon gayya.

Wani dan kabilar Tiv Farfessa Tor Irapor, ya sheda min cewar tun bayan da aka sami rikicin kwanan baya a jihar Benue ba'a tura jami'an tsaro ba zuwa yankin da aka kai harin na baya bayan nan.

Yanzu haka dai akasarin kauyuka da ke kusa da garin na Amusu sun zama kufayi, inda akasarin jama'a suka gudu suka bar gidajen su.

 

To sai dai acewar wani shugaban Miyetti Allah a jihar Filato Umar Abdullahi Dakare, kafa dokar haramta kiwo ne ya janyo ake cigaba da samun tashe-tashen hankula tsakanin fulani da kabilun jihar Benue, don kuwa kafin dokar ana samun zaman lafiya a jihar.