Rikici ya barke a yayin gudanar da zaben Kenya | BATUTUWA | DW | 26.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Rikici ya barke a yayin gudanar da zaben Kenya

Arangama tsakanin magoya bayan madugun 'yan adawa Raila Odinga da jami'an 'yan sandan Kenya a Kisimu ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda a wannan Alhamis a dai dai lokacin da ake sake gudanar da zaben shugaban kasa.

Wannan arangama dai tamkar wani mataki ne a bangaren 'yan adawan na haifar da cikas a zabukan da ke gudana a dukkan fadin kasar ta Kenya  a yAu. A garin Kisimu da ke yankin yammacin kasar, matasa magoya bayan Raila Odinga da ke jifa da duwatsu, sun yi kira ga jama'a da su kauracewa zaben. Kamar yadda wani mazaunin yankin James Onyango ya nunar. A Kisimu kamar dai sauran yankunan da madugun adawan yake da karfi, an amsa kiran da yai na kauracewa zaben shugaban kasar a yau. Matasan a yankunan dai na ci gaba da kona tayoyi akan tituna. A jawabi ga magoya bayansa a jiya a tsakiyar birnin Nairobi, Odinga ya ce ba zai shiga zaben na yau ba, bisa dalilan gaza cikanta bukatunsa na sauya jami'an hukumar zaben, bayan da kotun kolin kasar ta soke zaben watan Augusta.

A unguwannin Kibera da Mathare da ke birnin Nairobi dai, jami'an 'yan sanda masu kwantar da tarzoma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun mutane da suka tayar da rikici da sanyin safiyar yau.Saboda muhimmancin Kenyan a gabashin Afirka a fannin kasuwanci da sufuri da kuma kasancewar ta abokiyar huldar Turai ta fannin yaki da ta'addanci a Somaliya da yakin basasa a Sudan da Kudu da Burundi, hankali ya karkata kan yadda zaben na yau zai kasance.

Rahotanni na nuni da cewar duk fitowar da aka yi a yau domin gudanar da zaben bai kai wanda aka gudanar a baya ba, duk da cewar da sauran lokaci kamar yadda jagoran tawagar sa ido na kungiyar Tarayyar Afirka kuma tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ya nunar.Wajen mutane hamsin ne dai suka rasa rayukansu kawo yanzu a tarzomar da ta biyo bayan matakin kotun kolin kasar na soke zaben da ya gudana a watan Augusta. Duk da umurnin da Kotun ta bayar na sake gudanar da zaben bayan kwanaki sittin, madugun 'yan adawa Raila Odinga ya sanar da kauracewa zaben, saboda abun da ya kira " ba za'a gudanar da shi cikin adalci ba.

 

Sauti da bidiyo akan labarin