Rikici tsakanin sojojin Angola da Kwango | Labarai | DW | 19.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici tsakanin sojojin Angola da Kwango

Da alama har yanzu tsugune bata kare ba a kallon hadarin kajin da ake yi tsakanin kasashen Angola da kuma Jamhuriyar eimokaradiyyar Kwango.

Jami'an tsaron Angola sun saki sojojin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango 55 da suka kame a ranar Litinin din da ta gabata a yankin Kimongo dake kan iyakar kasashen biyu, inda suka tsaresu a kasar ta Angola.

Wani babban jami'in gwamnati daga gundumar Niari a Jamhuriyar Demokaradiyar Kwangon Jacques Mouanda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sun yi amfani ne da hanyar diplomasiya, kafin suka samu aka sako sojojin.

'Yan tawayen kasar Angola dake makwabtaka da Kwangon na da'awar cewa shi yankin na Kimongo mallakinsu ne.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe