Rikici tsakanin sojin Kwango da ′yan bindiga | Labarai | DW | 30.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici tsakanin sojin Kwango da 'yan bindiga

Sojin gwamnatin Kwango sun yi wani artabu da magoya bayan malamin addinin Kiristan nan na kasar Paul Joseph Mukungubila a birnin Lubumbashi da ke gabashin kasar.

Shaidun gani da ido sun ce rikicin ya samo asali ne bayan da dakarun gwamnatin suka afkawa majami'ai Mr. Mukungubila a tsakiyar garin na Lubumbashi wanda ke lardin nan na Katanga.

Wani jami'i a ofishin gwamnan lardin da ya tabbatar da wannan labarin, ya ce dakarun gwamnati sun dauki wannan matakin bayan da wasu 'yan bindiga da suka ce magoya bayan malamin addinin Kiristan ne dauke da makamai suka farwa gine-ginen gwamnati ciki kuwa har da filin saukar jiragen sama da hedikwatar gidan talabijin da na rediyo na kasar da ke Kinshasha wanda suka yi gwarkuwa da shi na dan wani lokaci.

Ya zuwa yanzu dai ba a tantance dalilin wannan rikici ba, yayin da a hannu guda rahotanni ke cewar kimanin mutane 40 ne aka tabbatar sun rasu a artabun, wadda ba a gano dalilin faruwarsa ba kawo yanzu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh