Rikici tsakanin Ghana da Kot Divuwar kan man fetur | Labarai | DW | 28.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici tsakanin Ghana da Kot Divuwar kan man fetur

Ghana da Kot divuwar sun fara takun saka da juna game da man fetur da ke kan iyakokinsu.

default

ƙasashen Ghana da kuma Kot Divuwar sun fara takun saƙa da juna bayan da aka gano rijiyoyin mai a gaɓar ruwan da ke haɗe ƙasashen biyu. Fadar mulki ta Yamousoukro da kuma takwararta ta Accra sun shigar da ƙara gaban kotun ƙasa da ƙasa ta duniya domin tantace iyakarsu da kuma ƙasar da ta mallakki rinjiyoyin.

Sai dai ɓangarorin biyu sun fara tattaunawa da juna a birnin Accra domin duba yiwuwar raba arzikin na fetur daidai wa daida tsakaninsu. Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta taɓa tantace iyakokin ruwa tsakanin ƙasashen kot divuwar da kuma Ghana ba, tun bayan samun 'yancin kan waɗannan ƙasashe da ga turawan mulkin mallaka na Fransa da kuma Ingila.

Rijiyoyin mai da kanfanonin Lukoil na Rasha da kuma Vanco Energy na Amirka suka gano a iyakokin ƙasashen biyu, sune waɗanda suka ƙunshi mai mafi yawa a yankin yammacin Afrika a cikin shekaru 10 na baya-bayannan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal 

Edita: Umaru Aliyu