Rikici tsakanin alƙalai da Shugaba Mursi | Labarai | DW | 24.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici tsakanin alƙalai da Shugaba Mursi

Alƙalai a Masar sun soki lamirin shugaban ƙasar Muhammad Mursi dangane da ƙarfin ikon da su ka ce ya bawa kansa wanda a cewarsu wani yunƙuri ne na nakasa tsarin shari'ar ƙasar.

zu: Bringt Mursi den Ägyptern Gerechtigkeit? NEW YORK, NY - SEPTEMBER 25: U Egyptian President Mohamed Mursi at the United Nations during a meeting at the General Assembly on September 25, 2012 in New York City. Over 120 prime ministers, presidents and monarchs are gathering this week at the U.N. for the annual meeting. This years focus among leaders will be the ongoing fighting in Syria with is beginning to threaten regional stability. (Photo by Spencer Platt/Getty Images)

Mohammed Mursi Präsident Ägypten

A wannan cikin wannan makon da mu ke shirin yin bankwana da shi ne dai shugaba Mursi ya sanya hannu kan wata doka da ta yi hani da ga kotunan ƙasar na su rusa majalisar dokokin ƙasar da yanzu haka ke aiki wajen rubuta sabon kundin tsarin mulkin ƙasar gami da sauya babban mai gabatar da ƙara da ya yi, to sai dai kotun ƙolin Masar ɗin a wata sanarwa da ta fitar a wannan Asabar ɗin ta ce wannan alƙibla da Mursin ya ɗauka karen tsaye ne ga tsarin shari'ar Masar kuma take-take na hana ɓangaren shari'ar ƙasar yin rawar gaban hantsi.

Wannan batu dai ya jawo kece na ce da kuma zanga-zanga musamman ma dai daga 'yan adawa da kuma alƙalai inda su alƙalan a garin a faɗin ƙasar su ka yi kiran da a shiga yajin a ƙasar baki ɗaya domin matsawa shugaba Mursi lamba da ya sauya tunani kan wannan doka da ya sanyawa hannu.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh