1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na daukar sabon salo a Birnin Kudus

Abdoulaye Mamane Amadou
May 9, 2021

A yayin da rikici ke ci gaba da ta'azzara tsakanin 'yan sanda da Falasdinawa a Kudus, Isra'ila ta mayar da martani kan mayakan Hamas a Zirin Gaza biyo bayan da ta zargi da harbo mata makaman roka daga yankin.

https://p.dw.com/p/3t9xA
Israel-Palästina | Neue Zusammenstößen in Jerusalem
Hoto: Oded Balilty/AP Photo/picture alliance

Rikici ya sake barkewa tsakanin 'yan sandan Isra'ila da Falasdinawa a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus a daidai lokacin da Falasdinawa ke ibadun neman yin gamon katar da daren lailatul kadri.

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a yankin Falasdinu, ta ce fiye da mutane 90 ne suka jikkata galibi kananan yara wadanda harbin harsashen roba da gurneti mai sa kwalla ya raunata.

Wannan dai shi ne rikici mafi muni da aka taba gani a 'yan shekarun baya-bayan nan a yankin, a ci gaba da ke Allah wadarai da matakin Isra'ila na korar Falastinawa don gina wa Yahudawa matsuguni a binrin Kudus da Falasdinawa ke yi.