Rikici na karuwa a Libiya bayan Kadhafi | Labarai | DW | 20.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici na karuwa a Libiya bayan Kadhafi

Duk da kiraye-kirayen kasashen duniya na a kawo karshen hare-hare tsakanin bangarori masu adawa da juna, tashe-tashen hankula na samun gindin zama a Libya.

Yayin da a wannan Litinin (20.10) marigayi shugaba Muammar Kadhafi ke cika shekaru uku da rasuwa, kasar Libiya na ci gaba da fuskantar tabarbarewar tsaro. Ko a jiya Lahadi wani sabon rikici ya barke a Benghazi lokacin da sojoji da ke mara baya ga gwamnati suka kaddamar da hari kan masu tada kayar baya. Mutane tara ne suka mutu, abinda ya kai adadin mutanen da suka rasu na baya-bayanan suka kai 75, kamar yadda likitoci suka bayyana.

Rikicin dai ya yi sanadin mutuwar wata mata, bayan wani harin bam da aka kai gidan tsohon janar Khalifa Haftar. A cewar likitoci a cibiyar kula da lafiya ta birnin Benghazi matar tana tafiya ne a gefen gidan na janar Haftar da wata karamar yarinya wacce ta samu raunuka a harin.

A ranar Asabar dai kasashe da suka hadar da Amirka da Birtaniya da Jamus da Faransa da Italiya sun bukaci da a gaggauta kawo karshen tashin hankali da ke ci gaba da samun gindin zama tsakanin masu goyon bayan gwamnati da mayakan sa kai.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe