Rikici na fada a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 25.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici na fada a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Sabuwar shugabar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fara neman hanyoyin kafa sabuwar gwamnati

Ana ci gaba da samun tashin hankali a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, duk da rantsar da sabuwar Shugaba Catherine Samba-Panza, wadda ta yi alkawarin hada kan al'ummar kasar, yanzu haka ta fara tattauna kan kafa gwamnati ta gaba.

A wannan Jumma'a da ta gabata wani tsohon minista na kasar Musulmi ya gamu da ajalinsa, bayan harin da wasu 'yan banga na Kiristoci suka kai masa a Bangui babban birnin kasar. Dr Joseph Kalite tsohon ministan kula da kiwon lafiya an kai masa hari lokacin da ya fito daga cikin motar haya a birnin Bangui.

A daren wannan Jumma'a sabon fada ya barke jim kadan bayan fara aiki da sabuwar Shugaba Samba-Panza ta yi, sojojin Faransa da Rwanda da na Burundi sun kutsa suka yi harbi cikin iska domin tarwatsa tsagerun suka farma wata ungula ta galibi Musulmai. Kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakyia ta fada rikicin tun lokacin da kungiyar 'yan tawaye Seleka ta galibi Musulmai ta kwace madafun iko a shekarar da ta gabata ta 2013.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba