Rikici na ci gaba da ritsawa da gabashin Ukraine | Labarai | DW | 14.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici na ci gaba da ritsawa da gabashin Ukraine

Rikicin da ke faruwa a yankin gabashin kasar Ukraine yana kara tabarbarewa.

An ci gaba da fafatawa da manyan makamai a rikicin da ya ritsa da yankin gabashin kasar Ukraine, abin da ya yi sanadiyar mutuwar karin mutum guda, inda tun farko fiye da mutane 20 suka hallaka.

Sabon rikicin ya barke yayin da motocin kayan agaji da Rasha ta tura suka nufi kan iyakar Ukraine.

A wani labarin majalisar dokokin kasar ta Ukraine ta amince da ayar dokar da ta bai wa gwamnati dama saka takunkumi da 'yan Rasha da kamfanonin kasar, wadanda ake zargi suna da hannu cikin rikicin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal