Rikici na ci gaba a yammacin Sudan | Labarai | DW | 30.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici na ci gaba a yammacin Sudan

Sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU a yankin Darfur sun tabbatar da mutuwar mutane da yawa bayan hare-hare ta sama da aka kai

Mutane masu yawa sun hallaka cikin hare-hare ta sama a Lardin Darfur na yammacin kasar Sudan mai fama da tashin hankali, kamar yadda dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen suka tabbatar a wannan Asabar.

Jami'in yada labarai na dakarun ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, sun samu bayanan daga mazauna yankunan.

Tuni kakakin rundunar sojan kasar Sudan ya musanta amfani da jiragen saman yaki wajen kai hare-hare, kuma babu wani fada da ya faru cikin yankunan, duk da cewa suna sane akwai 'yan tawaye.

Wani rahoton kwararru na Majalisar Dinkin Duniya cikin watan Febrairu ya ce, sojojin saman kasar ta Sudan na kai hare-hare da ke shafan fararen hula a Lardin na Darfur duk da musanta haka da gwamnati ke yi. Tun cikin shekara ta 2005 wani kudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya, ya nemi dakarun Sudan su kawo karshe amfanin da jiragen saman yaki a Darfur.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman