1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin arewacin Kamaru na kara kamari

Lateefa Mustapha Ja'afar BA
June 25, 2018

Rikici na kara Kamari a yankin arewacin Kamaru tsakanin jami’an tsaro da ‘yan awaren Ambazoniya da ke neman ballewa da ga Kamarun.

https://p.dw.com/p/30Gfm
Karte Kamerun Mamfe Bamenda Buea DEU
Rikici a yankin Bamenda na Kamaru

Rahotanni dai na nuni da cewa bayan binciken gida-gida a wani kauye da ke wajen birnin Bamenda mai suna Bambui da jami'an tsaro suka yi a karshen mako, a wannan Litinin din wata arangama ta barke tsakanin jami'an tsaron da 'yan awaren Ambazoniya da ke son ballewa daga Kamarun a garin Fundong da shi ma ke wajen birnin na Bamenda. Wakilinmu na Bamendan Baba Abdullahi ya shaida wa tashar DW ta wayar tarho cewa, an yi gagarumar arangama tsakanin jami'an tsaron da 'yan awaren a garin na Fundong, yayin da mazauna garin suka shige gidajensu tare da kllewa domin gudun abin da ka je ya zo. A yanzu dai hankula a tashe suke a arewacin Kamarun da ke yin magana da harshen Turancin Ingilishi.