Rikici a sansanin ′yan gudun Hijira | Labarai | DW | 02.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikici a sansanin 'yan gudun Hijira

Wasu 'yan gudun Hijira na cikin mawuyacin hali sakamakon rikici tsakanin 'yan Afganistan da 'yan Afrika a sansanin tsugunar da 'yan gudun hijira na Calais da ke kasar Faransa.

A halin yanzu mutane 22 ne kwance asibiti ciki kuwa har da  wasu 'yan kasar Iritiriya mutum 4 masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18, fadan dai ya samo asali ne ya yin layin karbar abinci lokacin da wa ni dan gudun hijira da ga Afganistan ya fara harbe harbe da bindiga.

Wani jami'i a sansanin ya shaidawa manema labarai cewar sansanin na Calais dai yayi zaman matsugunin sama da mutane dubu 10 masu aniyar tsallakawa Turai an kuma rushe shi tun a shekara ta 2016.

Sai dai har yanzu daruruwan 'yan gudun hijira sun yi kama guri zauna tare da kudurin shiga Turan ta barauniyar hanya. Jami'an tsaro sun kwatanta munin al'amarin da irinsa na farko da ya faru tun a lokacin da aka kirkiri sansanin a shekara ta 2015.