1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Rikici bayan daure jagoran 'yan aware

Ramatu Garba Baba
August 22, 2019

Rikici a yankin Bamenda da ke a yankin arewa maso yammacin Kamaru ya sake salo bayan da kotu ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga jagoran 'yan aware Julius Ayuk Tabe.

https://p.dw.com/p/3OKHD
Tshirt Francophonization
Hoto: Moki Kindzeka

Bayan yunkurin kwantar da hankulan 'yan kasa don mayar da kasar Kamaru turbar zaman lafiya da gwamnati Shugaba Paul Biya ke yi, sabon rikici ya kuma kunno kai a sakamakon hukuncin kotu na daure madugun 'yan aware Julius Ayuk Tabe, duk da haka masu gwagwarmaya na cewa ba gudu ba ja da baya a yunkurin son mayar da yankin na Ambazoniya a matsayin mai cin gashin kai..