1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a kungiyar tawayen Siriya

July 15, 2013

Rikicin cikin gida ya kunno kai a tsakanin kungiyar 'yan tawaye da ke yakar gwamnati a Siriya, wanda kuma ke barazanar raba kan 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/1985Z
Hoto: AFP/Getty Images

Babbar kungiyar 'yan tawayen Siriya ta bayyana bukatar kotun Musulunci ta gudanar da bincike kan mutuwar daya daga cikin manyan kwamandojinta, da ya rasa ransa a hannun dakarun sa kai na kasashen ketare, dake yakar gwamnati wadanda ke da kaifin kishin addini.

Wannan dai shine karo na farko da majalisar koli ta 'yan tawayen Siriyan da kasashen yamma ke marawa baya, ta yi wannan kira dangane da kisan Kamal Hamami da aka fi sani da Abu Bassir al-Ladkani, wanda ya janyo rarrabuwar kai tsakanin bangaren 'yan tawayen na Siriya dake da sassaucin ra'ayi da kuma bangaren masu kaifin kishin addini.

Wata majiya daga 'yan tawayen na Siriya ta bayyana cewa wanda ake zargi da aikata kisan Abu Ayman al-Baghdadi, ya buya kuma babu wata alama dake nuni da cewa Iraki ko kuma kungiyarsa ta Levent da ke Siriya wadda ke da alaka da al Qa'ida, za su mika shi ga kotun da ke arewacin garin Aleppo na Siriyan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Muahmmad Abubbakar