Rikici a Gaza na cigaba da kazancewa | Siyasa | DW | 30.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikici a Gaza na cigaba da kazancewa

Yayin da rikici a Gaza ke cigaba da kazancewa, Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da dakarin Izra'ila suka kai wata makaranta da mazauna Gaza suka fake.

Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce harin da dakarun na Bani Yahudu suka kai makarantar abin Allah wadai ne kasancewar ta shaidawa sojin na Izra'ila har sau 17 cewar mutanen da ke zaune a makarantar fararen hula ne da ke fakewa a cikinta don tsira da rayukansu sakamakon rikicin da ake yi.

Harin dai na makaratar ya yi sanadiyyar rasuwar kimanin Falasdinawa 15 wanda ke kwankwance a azuzuwan da ke makarantar lokacin da aka kai musu farmaki, kana masu aiko da rahotanni sun ce akalla mutane sama da dari ne suka samu raunuka wasu daga cikinsu munana.

Wata mata da ta tsallake rijiya da baya a harin ta ce ''muna kwance karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya lokacin da aka kai harin. Wasu daga cikinmu ma na dawowa daga masallaci sanda abin ya faru. Wannan abin da suke yi sam bai dace ba.''

Galerie - Tunnel Gazastreifen

Izra'ila na lalata hanyoyin karkashin kasa da Hamas ke amfani da su.

Faruwar wannan hari da ma dai cigaba da barin wutar da Izra'ila ke yi a yankin na Gaza ya sanya wasu kasashen duniya da wannan lamari bai yi wa dadi ba yanke huldar jakadancin da kasar. Kasashen da suka hada da El Salvador da Peru and Chile dai yanzu haka sun sanar da janye jakadunsu a wannan Larabar, yayin da a hannu guda Izra'ilan ta ce kasashen sun yanke gurguwar shawara domin kyautuwa ya yi a ce sun hada kai da ita wajen maganin an kawar da irin tada kayar bayan da 'yan Hamas ke yi.

Wannan batu dai na zuwa ne daidai lokacin da Izra'ila da ranar yau ta ce ta tsagaita wuta na tsawon sa'o'i hudu daga irin hare-haren da ta ke kaiwa yankin na Gaza saboda dalilai na jin kai, to sai dai lokaci kankani bayan fidda wannan sanarwar kimanin mutane 17 sun bakunci lahira yayin da sama da 100 suka jikkata sakamakon wani hari da dakarun na Izra'ila suka kai wani rukunin shaguna da ke Shaijiya a gabashin Gaza.

Gaza - einziges Kraftwerk brennt

Hare-haren Izra'ila a Gaza ya sanya yankin cikin rudani.

Ma'aikatar kiwon lafiyar a Gaza ta ce mutanen da wannan harin ya rutsa da su sun fito ne bayan da aka ayyana janye kai hare-hare na wani dan lokaci ba tare da la'akarin Izra'ilan na iya kaiwa ga kai hare-hare ba. Sojin Izra'ilan dai sun ce suna kai hari makmantan wannan ne saboda cigaba da bankado irin hanyoyin karkashin kasan nan da Hamas ke amfani da su wajen kai musu hari.

Guda daga cikin sojin Izra'ila ya ce ''mun samu hanya ne irin ta karkashin kasa da kuma rokoki da aka boye. An boye rokokin ne tsakanin bishiyu wanda hakan zai yi wuya a iya ganinsu in mutum na cikin jirgin yaki.''

Gabannin kai wannan harin dai Hamas dama ta sa kafa ta shure matakain da Izra'ila ta ce ta dauka na tsagaita, inda kungiyar ta ce ke ko kusa ba abu ne da za ta taba amince da shi ba don da wuya dakarun na Izra'ila su kai ga aiwatar da abinda suka fada.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin