1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawaitar asarar rayuka a Najeriya

July 26, 2018

Kungiyar kasa da kasa ta International Crises Group da ke sanya idanu a rikice-rikice, ta ce yawan rayuka da aka rasa a rikicin da ake alakanta shi da na makiyaya da manoma ya zarta na rikicin Boko Haram.

https://p.dw.com/p/327TZ
Nigeria Demonstration gegen Gewalt im Bundesstaat Zamfara
Zanga-zanagr neman kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a Zamfara, NajeriyaHoto: DW/Yusuf Ibrahim Jargaba

Kungiyar  ta International Crises Group dai ta bayyana hakan ne cikin wani sabon rahoto da ta fira, wanda ya nuna cewa a watanni shida na farkon wannan shekarar kawai sama da mutane 1300 aka hallaka a rigingimun da aka yi tsakanin makiyaya da manoma abin da ke zama kalubale ga kokarin wanzar da zaman lafiya da gwamnatin Najeriya ke yi. Ko da yake da dama ba su gamsu da wanna rahoton ba, da su ke ganin an wallafa shi ne ba tare da fahimtar asalin yadda rikicin yake ba, inda suka ce zai wahala idan hukumomi da irin wadannan kungiyoyi gami da wasu al'umma sun fahimci rikicin da ake alakanta shi da makiyaya da manoma.Tuni ma dai masana harkokin tsaro a Najeriyar suka fara tofa albarkacin bakinsu kan rahoton.

Cartoon Nigeria Nomaden-Bauer Konflikte
Hoto: DW

Zargin rura wutar rikicin

Sulaiman Aminu wani mai sharhi kan al'amuran tsaro ne a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar, a mahangarsa da ma ta wasu al'ummar yankin, ana rura wutar rikicin da sunan manoma da makiyaya ko kuma alakanta matsalar da wasu kabilu domin kunna wutar rikicin kabilanci da na addini. Wani abu da wasu ke ganin ya daure kai game da wannan rahoto shi ne yadda bai yi tsokaci kan abin da ke faruwa a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ba. Wannan ya sa wasu na ganin rahoton ya fi karkata ta gefe daya. Akwai kuma masu ganin irin rawar da wasu kafofin yada labarai ke takawa wajen bayar da rahotannin abin da ke faruwa, na dora alhakin hare-haren ga wani bangare kafin ma hukumomi su yi bincike su tabbatar. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta kai ga yin martani kan wannan rahoton ba sai dai ‘yan kasar na ci gaba da tafka muhawara a kai a kafafen sada zumunta na zamani, inda bangarorin ke tsarkake mutanensu abin da ke nuna rarrabuwar kawuna da ake da shi a kasar.