Rikice-rikicen Afirka sun dauki hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 17.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Rikice-rikicen Afirka sun dauki hankalin jaridun Jamus

Har yanzu fadi-tashi bai kare ba a kasashen Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya da Sudan Ta kudu, dzuk da shawarwarin neman sulhunta masu gaba da juna a kasashen

Jaridun na Jamus a wannan mako sun duba al'amura a dama da suka hada da halin da ake ciki a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya bayan murabus da shugaban kasar na rikon kwarya, Michel Djotodia yayi da kasar Sudan Ta Kudu, inda aka kasa samun ci gaba a shawarwarin neman zaman lafiya a yunkurin kawo karshen yakin basasa a kasar, har ya zuwa ga dokar hana auren jinsi daya da shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya sanya hannu a kasar.

Jaridar Der Spiegel ta duba Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya inda a karshen makon jiya, shugaban kasar na rikon kwarya, Michel Djotodia yayi murabus, a yunkurin taimakawa kawo karshen yakin basasa dake neman hadiye kasarsa. A sharhin na ta, jaridar Der Spiegel tace sai dai wannan mataki da ya dauka bai kawo karshen rikicin kasar ba. Ko da shike dubban yan sanda sun koma bakin aikinsu bayan da Djotodia yayi murabus, amma hakan bai hana a ci gaba da kaiwa kantuna da al'ummar musulmi, magoya bayan kungiyar yan tawaye ta Seleka hare-hare ba. A halin yanzu, kashi daya cikin kashi biyar na al'ummar birnin Bangui sun tsere a matsayin yan gudun hijira. A yayin da Faransa, tsohuwar uwargijiyar Jamhuriyar ta Afirka Ta Tsakiya take kokarin jan hankalin kasashen Turai su tura sojojinsu zuwa Bangui, kasashen Afrika, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung sannu a hankali hakurinsu yana karewa ne da abin dake gudana a Bangui. Shugabannin kasashen tsakiyar Afirka a taronsu a Ndjamena, bayan matsa lamba ga Michel Djotodia yayi murabus, sun kuma nunar a fili cewar ba zasu ci gaba da zura idanu suna ganin halin da ake ciki yana kara muni a kasar ba.

Südsudan Militär 14.1.2013

Yakin basasa a Sudan Ta Kudu

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland ta duba ziyarar Pirayim ministan Japan, Shinzo Abe ne a nahiyar Afirka, inda tace Japan ita ma ta shiga tserereniyar neman angizo a nahiyar Afrika. Jaridr ta nuna cewar tuni gwamnati a Tokio take lura da take-taken China da kara shisshiginta a nahiyar Afirka. Yanzu kuwa China din ta sami abokiyar takara, inda Shinzo Abe yake tafe da kwangiloli na kudi miliyoyi dubbai domin taimakawa nahiyar. A ziyarar tasa, Abe yayi tattaki zuwa kasar Cote d'Ivoire, inda yake fatan bayan rikicin siyasa da ta shiga, yanzu zata zama kofar da Japan din zata yi amfani da ita domin shiga nahiyar Afirka baki daya. Daga baya Pirayim ministan ya yada zango a Mozambik da Habasha.

Jaridar Tageszeitung ta tabo halin da ake ciki a kasar Sudan Ta Kudu, inda yakin basasa ya barke sakamakon gaba tsakain shugaban kasa, Salva Kiir da tsohon mataimakinsa, Riek Machar. Duk da shawarwarin neman sulhu a Addis Ababa, babu alamun bangarorin biyu masu yaki da juna zasu amince da tsagaita bude wuta. Garin Bentiu babban birnin lardin Unity mai arzikin man fetur, ya zama dandalin dauki a dadi a wannan mako, inda shaidu suka ce an lalata garin gaba daya, kuma mafi yawan mazauna cikinsa sun tsere a matsayin yan gudun hijira.

Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A karshe jaridar Die Zeit ta duba dokar hana auren jinsi daya a Najeriya da shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya sanya hannu kanta. Jaridar tace shin akwai wani ci gaba a kokarin baiwa tsiraru yanci ko hakkinsu a duniya baki daya? A Najeriya, inji jaridar, tun daga wannan mako, duk wadanda aka same su da laifin kasancewa masu neman jinsi daya, zasu sha hukuncin daukin akalla shekaru 14 a gidan kaso. Hakan dai wani mataki ne na kokarin tauye hakkin tsiraru, musamman masu neman jinsi daya da kuma nuna kyama ga kasashen yamma da al'adunsu.