Rigingimu na shafar noma a Najeriya | Zamantakewa | DW | 06.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rigingimu na shafar noma a Najeriya

Manoma Doya a yankunan da suka fuskanci tashe-tashen hankula a wasu kauyukan da ke kan iyakokin jihohin Benue da Nasarawa, sun bayyana damuwa sakamakon matsalar tsaro da ta sanya suka gujewa gonakinsu.

Nigeria Menschenhandel Bundesstaat Benue (DW/K. Gänsler)

Saiwar Doya baje a wata kasuwa a Benue, yayin da masu saye ke kallo

Koda yake yanzu ana iya cewa an soma samun saukin hare haren da suka yi kamari kwanakin baya a Benue, to amma dai manoman Doya tare da wadanda ke kasuwancinta, sun soma kokawa kan yadda rigimar ta jefa su cikin mawuyacin hali. Wasu manoman Doyan a jihar wadanda suka tsallake kan iyaka zuwa Nasarawa, sun nuna damuwa kan cewa yanzu basu da damar komawa gonakinsu. Wannan matsala dai ta shafi 'yan kasuwan Doya, don haka nema Alh Isa Ibrahim wani manomi kuma mai sayar da Doya a kasuwar Doya da ke Agyaragu cikin jihar Nasarawa, ya shaidar da cewar dole yanzu ta sanya manoman ke sauya lokutan da suke shukin doya, ba kamar can baya ba. 

Akwai dai alamun dake nuna cewar wannan matsala ta rashin tsaro ka iya janyo karancin abinci mussaman ma Doya a Najeriyar, sakamakon yadda manoman yankunan karkara ke gujewa gonakinsu. Amma shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Nasarawa Umaru Tanko Tunga, ya ce koda yake rigimar ba a Nasarawa aka yi ba, amma majalisar dokokin jihar tuni ta dauki mataki. 

Masana harkokin gona sun yi la'akarin cewar muddin gwamnatin Najeriya na son cimma kudurinta na soma fitar da doya zuwa kasashen duniya nan gaba, to kamata ya yi ta kara azama ta fuskar tsaron rayukan wadannan manoma da ke zage wa ayyukan gona a kowace shekara wajen samar da abinci.