Ricikin Ukraine na ci gaba da lamshe rayuka | Labarai | DW | 20.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ricikin Ukraine na ci gaba da lamshe rayuka

Mutane fiye da 30 sun hallaka a sabon rikicin da ke gudana tsakanin gwamnati kasar Ukraine da kuma masu fafitikar ballewa na gabashin kasar.

Mutane 34 sun hallaka yayin sabon fada da ya barke tsakanin 'yan aware masu goyon bayan Rasha da kuma dakarun kasar Ukraine a garin Donetsk na gabashin kasar ta Ukraine.

Rahotannin sun ce an yi fafatawan a gabashin Donetsk. Wannan yayin da ake neman hanyoyin siyasa na magance rikicin gabashin kasar ta Ukraine, inda Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce zai yi karin wata ganawa kan rikicin da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe