Renamo ta yi watsi da tayin tattaunawa da gwamnatin Mozambik | Labarai | DW | 05.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Renamo ta yi watsi da tayin tattaunawa da gwamnatin Mozambik

Duk da cewa shugaba Guebuza na Mozambik ya nuna cewa ɓangarorin za su mutunta ƙasa ne idan sun tattauna, Renamo ta ce ba za ta lamunci harin da aka kai mata ba.

Foto Armando Guebuza 1. Titel: Armando Guebuza, Präsident von Mosambik 2. Bildbeschreibung: Armando Guebuza, Präsident von Mosambik 3. Fotograf: Romeu da Silva 4. Wann wurde das Bild gemacht: Juli 13 5. Wo wurde das Bild aufgenommen: Maputo/Mosambik 6. Schlagwörte: Mosambik, Maputo, Staatsrates von Mosambik, Armando Guebuza, Präsident von Mosambik

Armando Guebuza shugaban ƙasar Mozambik

Kungiyar tawayen Mozambik, da ta farfaɗo wato Renamo ta yi watsi da tayin da gwamnati ta miƙa mata wannan Talatar (05. 11. 13), na gudanar da tattaunawa ta kai tsaye domin shawo kan yanayin da aka shiga yanzu.

Gwamnatin da ke ƙarƙashin jagorancin Frelimo ta gayyaci babban abokin hamayyarta Afonso Dhlakama zuwa birnin Maputo ranar takwas ga wannan wata na Nuwamba, domin ya tattauna kai tsaye da shugaba Armando Guebuza.

Sai dai jim kaɗan bayan haka, Renamo ta ce ba za ta amsa wannan gayyata ba. Ga 'yan Mozambik da dama, wannan lamari na tunatar dasu kan yaƙin basasar da aka ɗauki shekaru 16 ana gwabzawa tsakanin ɓangarorin na Frelimo da Renamo.

Shugaba Guebuza ya ce yana so a gudanar da tattaunawar ce domin mutunta mutanen Mozambik. Sai dai 'yan tawayen na zargin gwamnatin da ƙaddamar da hari kan maƙarfafarsu da ke tsakiyar Mozambik, abin da suka ce ba za su lamunta ba.

A halin da ake ciki yanzu, tattaunawa ta kai tsaye tsakanin jagororin ɓangarorin biyu ne kaɗai ake gani zai warware matsalar, tunda tattaunawar da aka shafe watanni ana yi tsakanin Renamo da gwamnatin ƙasar bata haifar da ɗa mai ido ba.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh