1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Redio mai zaman kanta ta farko ta fara aiki a ƙasar Guinée

Yahouza S.MadobiAugust 16, 2006

Guinee Nostalgie FM , redio farko mai zaman kanta ta fara watsa shirye-shirye a birnin Conakry.

https://p.dw.com/p/Btyi
Hoto: Daniel Hierschler

Ƙasar Guinee Conakry, ta shiga sahun ƙasashen Afrika , masu cin moriyar tsarin mulkin demokradiya, ta fannin girka gidajen rediyoyi masu zaman kann su.

A wannan laraba ne, gidan Redio na farko mai kan sa, mai suna Nostalgie Guinee ya fara watsa shirye shiryen sa, ta zagon FM, a babban birnin Conakry.

Nostalgie FM ,na da rassa a ƙasashe da dama, na yammacin Afrika.

Rahotani daga ƙasar sun ce, al´umma na cike da raha ,da farin ciki. Su na matuƙar murna, ta yadda daga yanzu, su ka samu yancin murɗa rediyoyin, su cenza tasha, domin sauraran wani sauti, daban da wanda su ka saba sauraro, tun fiye da shekaru 50, da su ka gabata, inda gidajen rediyoyin ƙasar baki ɗaya, su ka maida aƙida ta fannin yaɗa manufofin siyasar gwamnati.

Makale Sumah, wani ɗan jarida a birnin Conakry, ya bayyana cewar tun da sabuwar rediyon ta buɗe, ya fara laluben tashoshi, daga Redio Nostalgie, zuwa rediyoyin gwamnati.

Saidai wasu al´umomnin ƙasar sun fara ƙorafin cewar redio ba zata fara watsa labarai ba, cikin gaggawa.

Dakartan Nostaligie Guinee, Djibril sakho, ya tabbatar masu da cewar, shirye shiryen da ka fara yanzu, tamkar gwanji ne, kuma nan da ɗan lokaci ƙalilan redion, zai fara labarai a halshen faransanci, da sauran manyan halsuna na ƙasa.

Tun watan juyi da ya gabata ministan sadarwa Abubakar Sylla, ya bada izinin watsa shirye shirye, ga gidajen rediyoyi masu zaman kann su, su guda 3, da su ka haɗa da Radio Nostalgie Guinee, FM radio liberte, da kuma Radio Soleil FM.

An tace wannan ridiyoyi 3, daga jerin takardun neman izini guda 10.

Hukumar sadarwa ta kasa ta shaida cewar zata ci gaba da nazarin sauran takardun, kuma ba mamaki, nan da wani lokaci, a ƙara samun wasu gidajen rediyoyin masu zaman kansu, da za su fara watsa shirye shirye a ƙasar Guinee.

Minista Abubakar Sylla, ya nunar da cewa, gwamnati ta yanke shawara amincewa da buɗa tashoshin redioyi masu zaman kan su, domin cimma burin ta, na yaɗa demokardiya cikin ƙasa, da kuma faɗakar da jama´a a kan al´ammura daban-daban na rayuwa.

A game da haka, ministan yayi kira ga magabatan sabin rediyon, da su gudanar da ayyuka, cikin kare haƙƙoƙin ƙasa, da na yancin faɗin albarkacin bakin yan jarida.