Rayuwa ta koma kamar yadda aka saba a Zirin Gaza | Labarai | DW | 22.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rayuwa ta koma kamar yadda aka saba a Zirin Gaza

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga Isra'ila da ƙungiyar Hamas da su girmama shirin tsagaita wuta.

Rayuwa ta koma yadda aka saba a Zirin Gaza biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra'ila da Hamas, bayan sun shafe kwanaki takwas suna fafatawa. A wannan Alhamis titunan birnin Gaza sun cika da motoci da jama'a, inda kowa ke gudanar da harkar gabansa yayin da ake ci gaba da aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar. Falasɗinawa a Zirin Gaza sun kwashe daren Larabawa suna shagulgulan tsagaita wutar. A halin da ake ciki kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira ga Isra'ila da kuma ƙungiyar Hamas da su girmama yarjejeniyar da suka ƙulla ta dakatar da yaƙin. A cikin wata sanarwa kwamitin sulhun ya roƙi sassan biyu da su ɗauki shirin tsagaita wutar da muhimmanci. Sannan a lokaci ɗaya kuma kwamitin ya yi kira ga gamaiyar ƙasa da ƙasa da ta ƙara yawan taimakon gaggawa ga al'ummar Zirin Gaza. Yanzu haka Jamus ta yi wa Falasɗinawa alƙawarin ƙarin taimakon Euro miliyan 1.5 don samar da magunguna ga Zirin Gaza. Ƙasashen duniya sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu