Rayuwa cikin fargaba a Kidal da ke Mali | Siyasa | DW | 28.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rayuwa cikin fargaba a Kidal da ke Mali

Shekara guda kenan da dakarun Faransa da na Kungiyar Tarayyar Afirka suka ayyana samun nasara a kan 'yan tawayen da suka mamaye yankin arewacin kasar.

Birnin Kidal da ke yankin arewacin Mali dai na ci gaba da kasancewa mai hadarin gaske saboda ta'asar da 'yan tawayen Kungiyar MNLA ke ci gaba da tafkawa, musamman ma a kan 'yan jaridun ketare, bayan kisan wasu 'yan jaridun Faransa guda biyu da ake zargin wata kungiyar mayakan da ke da alaka da al-Qa'ida ta yi a shekarar da ta gabata. Sauran mazauna birnin na Kidal irinsu Tiefolo Coulibaly dai suka ce suna cikin fargaba:

Ya ce "To, ganin yanayin da ake ciki a wannan birni na Kidal, wanda ba kowa a cikinsa, don haka komi na iya tarwatsewa a ko wane lokaci ganin irin abubuwan suka wakana. Ganinma abin da ya faru da banki, tunda mun ga banki ya tarwatse a gabanmu, don haka muna cikin yanayi ne na rashin tsaro da kwanciyar hankali ne"

Kungiyar 'yan tawayen MNLA ce ke kula da harkokin tsaro a birnin na Kidal, maimakon dakarun gwamnatin Mali, ko kuma na Majalisar Dinkin Duniya, abin da mazauna birnin suka danganta da cewar, ya samo asali ne tun bayan yakin da a baya bayannan Faransa ta jagoranta a kasar. Shi ma Coulibaly yana da irin wannan matsayin:

Ya ce "Lalle gaskiya ne kungiyar MNLA ana iya cewa tana da alaka da Faransa. Ai an jima ba a ga 'yan kungiyar ba, in banda lokacin da Faransa ta zo ta shiga tsakani ba. Don haka mu a ganinmu kungiyar MNLA wani boyayyen hannu ne na Faransa. Mu a yanzu abin da muke son mu bada shawara akai shi ne kawai Faransa da sauran kasashen duniya su nemi hanyar magance bukatun al'ummomin da ke wannan wurin. "

Bewegung Befreiung Azawad Gebiet Tuareg Mali MNLA Afrika Mali

Mayakan tawaye na Azawad

Ta ce "mu bamu san yaki ba. Muna zaune ne cikin kwanciyar hankali, sai ma ka kwanta a cikin fili, babu wanda ya damu da kai ba, ko ya tambayeka me kake yi ba, amma yanzu gashi nan kowa yana cikn yanayi na tsoro."

Ta ce" mu a ganinmu wadanda ake kira 'yan Jihadin anan ba su da laifi don a lokacin su, ba a sata, ba a zuwa a fasa mana shago, ko wane abin ka aka sace, da zarar ka je wurin shugabansu, za a nemo maka. Don haka a lokacinsu muna zama cikin kwanciyar hankali, amma kungiyar MNLA su ne suka bugemu, su ne suka sace mana kayayyakinmu, kuma suka sace mana mutanenmu. Kai ko wace ta'asa ma su ne suka tafka."

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin