1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin matasa a siyasar kasar Kamaru

October 9, 2018

A yayin da zaben shugaban kasa ke kara matsowa a kasar Kamaru, Za a iya cewa wannan shi ne karo na farko da wani matashi ya fito takara tare da goyon bayan matasan kasar, domin fafatawa da shugaban kasar Paul Biya.

https://p.dw.com/p/363ww
Kamerun Präsidentschaftswahl Wahlkampf
Hoto: DW/K. Gänsler

Shugaba Paul Biya da ke da shekaru 85 a duniya ya dare kan karagar mulki tun cikin watan Nuwambar shekara ta 1982. Matashi Cabral Libii dan shekaru 38, shi ne mafi karancin shekaru a jerin´yan takar shugabancin kasar a zaben da ke tafe ranar Lahadi bakwai gha wannan wata na Oktoba da muke ciki. Matasa irinsu Jules Henry Mbock shugaban kungiyar “11 millions Voters” da Cabral Libii ya kafa a Douala, kungiyar da ke wayar da kan matasa kan yin rijista da kuma kada kuri'a domin kawo sauyin da suke bukata, na da ra'ayin cewa da wannan gangamin wayar da kan ne kadai za su iya kai wa ga cimma burinsu na kawo sauyi a dimukuradiyyar kasar yana mai cewa:

China Peking - Kameruns Präsident Paul Biya
Shugaba Paul Biya na kasar KamaruHoto: picture-alliance/AP Photo/L. Zhang

''A kullum ina cewa wannan shi ne zabe na farko da zai gudana a kasar Kamaru, domin a baya babu wani zabe da ake yi sai murdiyya kawai. Amma a makwannin da suka gabata mun shirya taron karawa juna ilimi, domin wayarwa da matasa kai kan abin da ake nufi da zabe da mahimmancinsa, a da babu mai zuwa nan amma yanzu mutane har 600 suka halarci taron'''.

Wadannan matasa dai sun nuna bajinta, wajen kirkirar wata na'ura mai suna "Electra Transparency," da ke tantance sakamakon zaben da zarar an aza mata tsarin jadawalin zaben a kanta wadda kowa da kuma ko wacce jam'iyya za su iya amfani da ita."

Kamerun Wahlkampf in Yaounde 2011 | Anhänger von John Fru Ndi
Yakin neman zabe a YaoundeHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

A nasa bangaren Cosmas Cheka da ke zaman masani kan hakokin shari'a, kuma malami a fannin nazarin shari'ar a jami'ar  Yaoundé ta biyu, ya bayyana cewa matasan na da karsashi kuma sun shiryawa zaben, sai dai duk da haka akwai kalubale na rashin yin rijistar zabe yana mai cewa duk da gangamin da suke yi a kafafen sada zumunta, zai wahala su iya yin tasiri a sakamakon zaben..

Kamaru dai na zaman kasar da tafi yawan matasa a nahiyar Afirka, domin kuwa kaso 62 cikin 100 na al'ummar kasar miliyan 25 matasa ne. Wani kiyasi da Kungiyar Kwadago ta Kasa da Kasa Internatioanal Labour Organization ta fitar, ya nunar da cewa sama da kashi takwas na matasan da ke da shekaru 15 zuwa 24 a Kamaru ba su da aikin yi.