1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar da matasa ke takawa a zaben Jamus

September 8, 2017

Jam'iyyun siyasa na tarayyar Jamus sun shiga zawarcin kuri'un matasa gadan-gadan don samun tabbacin rinjaye a zaben 'yan majalisar tarayyar na 24 ga watan Satumba mai zuwa.

https://p.dw.com/p/2jb14
wahlgang.de
Hoto: wahlgang.de

Matasan Jamus da ke kada kuri'a a zabubbuka daban-daban ba su taka kara sun karya ba idan aka kwatanta da wadanda ke da shekaru 50 zuwa 70. Alkalumma sun nunar da cewar da ratar akalla maki goma daga cikin 100 tsakanin adadin wadanda suka fara shekaru da masu jin jini a jika a fannin yawan kada kuri'a. Klaus Hurrelman, masanin halayyar dan Adam, kuma daya daga cikin matasa da aka fi ji da su a Jamus a fannin bincike-bincike ya ce "masu jin jini a jika na ganin cewar tsofoffi za su fi zaban dan takarar da ya fi dacewa.Kididdiga ta nunar da cewar magoya bayan jam'iyyun CDU/CSU da SPD da FDP da Linke na da kusan shekaru 60 kowannensu."

Deutschland TV Duell Merkel - Schulz
Hoto: Reuters/WDR/H. Sachs

An fara samun matasan da ke da kasa da shekaru 30 da ke shiga jam'iyyun siyasa a Jamus domin a dama da su, lamarin da an shafe shekaru ba aga irinsa ba, sai dai ba a tantance ko zaben 'yan majalisa da ke tafe ne ya daukar musu hankali ba, ko sun amince ne da manufofin jam'iyyun da suka runguma ba. Masanin zamantakewa Klaus Hurrelmann ya ce siyasa na ci gaba da zama wata dama ga matasa ta bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa. Matasan Jamus suna sane da irin mummunan tasirin da rashin shigar masu jin jini a jika harkokin zabe Birtaniya ya yi, inda a karshe ficewa daga kungiyar gamayyar Turai ta samu rinjaye, lamarin da ya saba wa ra`ayin galibi daga cikinsu.