Rashin wadatar tallafin dakile bakin haure daga Afirka
September 27, 2024Wani rahoto da masu binciken kudi na kungiyar tarayyar Turai EU suka fitar, ya nuna cewa tallafin da asusun kungiyar ya bai wa nahiyar Afirka don aikin dakile kwararar bakin haure zuwa Turai bai wadatar ba, la'akari da yadda tallafin ya gaza yin katabus wajen agazawa al'umma don inganta rayuwarsu da kuma kare 'yancinsu a nahiyar.
Kungiyar tarayyar Turai EU ta kaddamar da asusun tallafin ne a shekarar 2015, a wani mataki na magance matsalolin 'yan gudun hijira tun daga tushe da ke kara zafafa, har ma ake samun kamari ta fuskantar kwararar bakin haure daga Afirka zuwa Turai, to amma kafin shirin ya ci Talata da Laraba ya fara cin karo da tasgaro, bayan da masu binciken kudi na kungiyar suka yi zargin cewa an sauka daga kan doron manufar kafa asusun.
Haka zalika rahoton ya ce kudin ya yi karanci matuka, idan aka yi duba da irin bukatun da ake da burin cimma wa a kai, da suka karade yankunan Afirka uku, kama daga Sahel da Tafkin Chadi, zuwa Kahon Afirka, da kuma Arewacin Afirka, wadanda suka kunshi kasashe 27 na nahiyar.
Bettina Jakobsen na daya daga cikin jagoron kungiyar ta EU da suka gudanar da wannan bincike, da ke nuna cewa an sauka daga kan tsarin da aka kafa shi tun da fari.
''Yanzu da mu ke tunkarar karshen wa'adin da aka debar wa aikin asusun tallafin na Euro biliyan biyar, abin takaici sai mun sake maimaita abubuwan da muka gudanar shekarun baya, kuma babban abin damuwar ma a matsayinmu na masu binciken kudi shi ne kwata-kwata ma ba a kashe kudin a bangaren da aka tsara tun asali ba, sai wasu wurare marasa muhimmanci. Babu kuma wani tasirin a zo a gani da muka gani game da aikin kawo karshen kwararar bakin haure zuwa Turai, babu wani kokarin kare hakkin mutane babu wani katabus ta fuskar samar da aikin yi ga jama'a''.
Rahoton na EU ya nuna cewa an kasafta kudin ne zuwa fannoni hudu, inda aka kebe kashi 17 cikin 100 ga bangaren samar da ayyukan yi ga jama'a, sai kashi 28 cikin 100 ga fannin da ya shafi gina yankunan al'umma. Kashi 31 cikin 100 an tsara kashe kudin ne kai tsaye ga shirin dakile kwararar bakin haure zuwa Turai, yayin da aka shirya kashe kashi 22 cikin 100 na kudin ga ayyukan sasanta rikice-rikice tsakanin al'umma, tare da tabbatar da shugabanci na gari a tsakaninsu.
Niels Keijzer babban jami'in bincike na cibiyar bunkasa ci gaban al'umma ta IDOS da ke nan Jamus, ya bayyana shirin tamkar an sayo kare ne don haushi, amma ya bige da tunkuyi.
''An yi amfani da kudin wajen dashen itatuwar Kirsimeti, wadanda ba su da wata alaka da ta shafi magance matsalar tururuwar shiga Turai da mutane ke yi, don haka akwai gagarumin kalubale a gaba, na yadda ya kamata a ce an gudanar da shirin cikin nasara. Kalli dai yadda haka siddan aka narkar da kudi ga wani gidan Rediyo a Libya, wanda kade-kade kawai yake saka wa, maimakon mayar da hankali wajen janyo ra'ayin matasa kan abin da aka sanya a gaba na bunkasa rayuwarsu''.
EU ta dauki gabarar gudanar da daruruwan nazarce-nazarce da za su samar da mafita kan tarin matsalolin da suka addabi nahiyar Afirka, kama daga rikice-rikicen cikin gida da ke haifar da 'yan gudun hijira da kuma kwararar baki masu neman mafaka a Turai, da nufin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar.