Rashin tsaro na korar baki a Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 10.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rashin tsaro na korar baki a Afirka ta Kudu

Daruruwan 'yan kasashen waje sun yi zaman dirshan a harabar ofishin kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Cape Town, inda suke neman hukumomi su mayar da su kasashensu na asali.

Sama da masu neman mafaka 250 a Afirka ta Kudu na neman hukumomi su gaggauta fitardasu daga kasar saboda rashin tsaro. Matakin da bakin suka dauka na da nasaba da munanan hare-hare kin jinin baki da ya faru watanni da suka gabata.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a kasar ba su yi martani kan wannan sabuwar dambarwa ba tukuna. Kasashen Afirka da dama ciki har da Najeriya sun yi Allah wadai da yadda aka yi ta kashe baki da lalata dukiyarsu a Afirka ta Kudu.