1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya ta shiga matsalolin tsaro

Lateefa Mustapha Ja'afar SB
May 14, 2021

Halin rashin tsaro da rashin tabbas a Najeriya da batun yunwa a Madagaska da kuma allurar riga-kafin corona a Afirka, sun dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3tOPg
Symbolbild Nigeria Polizei
Hoto: imago/Xinhua

Jaridar die tageszeitung da ta rubuta sharhinta mai taken: "Shin Najeriya ta kama hanyar rugujewa?" Jaridar ta ce tashin hankali ya mamaye kasar, an ma daina ganin babban birnin kasar Abuja a matsayin tudun mun tsira kan rashin tsaro. Shugaban kasar Muhammadu Buhari da a yanzu ba ya tunani kan komai, na kara shan suka. Ta ce tun a shekara ta 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan madafun iko, sai dai babu wani abu da ya sauya. Dalili shi ne: Kasar ta jima cikin halin rashin tsaro da tashe-tashen hankula. A yankin tsakiyar kasar, akwai rikicin Fulani da makiyaya a yankin Kudu maso Gabashi kuwa rundunar sojoji da ta 'yan sanda na yakar kungiyar masu dauke da makamaia da ke son ballewa daga Najeriya, masu sacewa tare da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun addabi yankin Arewa maso Yamma yayin da yankin Arewa maso Gabas ke fama da 'yan ta'addan Boko Haram da a kullum ke sababbin hare-hare. A farkon wannan wata na Mayu, iyayen daliban da aka sace a makarantu, sun gudanar da zanga-zanga a Abuja fadar gwamnatin kasar da kuma jihar Kaduna inda aka kwashe daliban cikin watannin Maris da Afrilun da ya gabata.

Nigeria | Ein gefallener Staat | Karikatur
Hoto: Abdulkareem Baba Aminu/DW

Karin Bayani:Mayar da kayan tarihin Najeriya daga Jamus ya dauki hankalin jaridun Jamus

Shugabannin addini da na kabilu a kasar na gargadi kan yiwuwar rushewar kasar ko kuma fada wa cikin yaki. Abin da shugaban Kabilar Yarabawa Gani Adams ya ce ba za a taba yafe wa Buhari ba idan har hakan ta kasance.Wasu kungiyoyin farar hula 127 a kasar da suka rasa mambobinsu har 2000, a rukuni na farko na wannan shekara ta 2021 sun bukaci a tsige Buhari daga kan karagar mulki in har ba zai iya kawo karshen zubar da jini ba. Sun shirya gudanar da zanga-zanga da zaman makoki a ranar 28 ga wannan wata na Mayu, domin tunawa da  wadanda suka rasa rayukansu a abin da suka kira mummunan yanayi. Kamar kullum Buhari ya mayar da martani ga wadannan zarge-zarge ta bakin mai magana da yawunsa, inda ya gargadi matasa da kada su bari wasu su yi amfani da sua wajen ciwa kasarsu dunduniya.  A farkon watan Janairu ne Buhari ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar, sai dai har yanzu ba ta canza zani ba.

Madagaskar I  Hunger
Hoto: RijasoloAFP/Getty Images

Amfanin gona da dama sun lalace in ji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ce a Madagaska sama da mutane miliyan guda na fama da matsalar yunwa. Shekaru uku babu ruwan sama. Ta ce yankin kudancin Madagaska na fuskantar barazanar fari da ba a samu irinsa ba a shekaru 40 din da suka gabata. Wannan kadai babbar matsala ce, baya ga a wannan shekarar coronavirus ta kawo nakasu ga bangaren yawon bude idanu, abin da ya janyo nakasu ga bangaren kudin shiga da kasar ke samu a wannan fannin. Shirin samar da abinci na Majaliksar Dinkin Duniya, ya bayyana cewa mutane dubu 14 na cikin halin tasku. Kungiyar Likitoci na Gari na Kowa Doctors Without Borders, sun bayyana cewa yaro guda cikin yara biyar na fama da matsalar rashin abinci. A yankin Amboasary al'umma na yin tafiyar kusan yinin guda kafin su samu ruwan sha.  Madagaska na zaman kasa mafi talauci a nahiyar Afirka, inda kaso 90 al'ummar kasar da yawanta ya kai miliyan 26 ke rayuwa a kasa da dalar Amirka daya. Sama da rabin yaran kasar na fama da rashin abinci mai gina jiki.

Ghana Accra | 37 Militärkrankenhaus: Nana Akufo-Addo wird geimpft
Hoto: Information ministry of Ghana

Ba mu karkare da sharhin jaridar Süddeutsche Zeitung mai taken: Can kasa cikin jeri. Jaridar ta ce koda a kasashen da Ghana da Ruwanda da  ke zaman abin koyi, kaso uku kacal na al'ummar kasar suka iya yi wa riga-kafi. A farkon watan nan na Mayu, kason farko na allurar Biontech/Pfizer ya isa filin jiragen sama da ke birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, kasar da ta fi kowacce fama da annobar a Afirka da kuma ta iya yi wa kaso daya kacal na al'ummarta riga-kafin. Yayin da a kasashen Turai da Amirka ake fatan kawo karshen yin allurar ga al'umma zuwa lokacin hutun bazara, a nahiyar Afirka babu abin da ya sauya dangane da yaki da annobar.