Rashin tabbas kwana daya bayan masu zabe a Girka sun yi fatali da jadawalin ceto tattalin arzikin kasar | Labarai | DW | 06.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rashin tabbas kwana daya bayan masu zabe a Girka sun yi fatali da jadawalin ceto tattalin arzikin kasar

Ministan kudin Girka Yanis Varoufakis ya yi murabus daga bakin aiki, duk da nasarar da gwamnati ta samu yayin zaben raba gardamar kasar.

Masu zabe a kasar Girka sun yi fatali da matakan tsuke bakin aljihu na kungiyar Tarayyar Turai, da masu bai wa kasar rance suka shata. Yayin zaben raba gardama da ya gudana a wannan Lahadi da ta gabata, kashi 60 cikin 100 na masu zaben sun nuna rashin amincewa, sannan kimanin kashi 39 suka amince da shirin na ceto tattalin arziki.

Firaminista Alexis Tsipras na kasar ta Girka ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tattaunawa da masu ba ta bashi, kuma yana sane da cewa kuri'ar ba ta bayar da damar ficewa daga kasashen Turai.

Firaminista Tsipras ya kara da cewa:

"Mutane da yawa za su yi watsi da muradun gwamnati. Amma babu wanda ya isa ya yi watsi da muradun mutanen da suka dauki makomar su a hannunsu."

Shugabannin kasashen Turai masu amfani da kudin bai daya na Euro za su gana gobe Talata, domin tattauna sakamakaon zaben raba gardama na kasar ta Girka.

A kuma halin da ake ciki ministan kudin kasar ta Girka Yanis Varoufakis ya yi murabus daga bakin aiki.