1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas game da wanda ya kai harin Berlin

Ahmed Salisu
December 20, 2016

Hukumomi a Jamus sun ce mutumin da ake zargi da kai harin kasuwar nan ta Kirsimeti da ke babbab birnin kasar wato Berlin a daren Litinin din da ta gabata ya ce ba shi da hannu a wannan hari da aka kai.

https://p.dw.com/p/2Uawm
Deutschland Anschlag mit LKW auf Weihnachtsmarkt in Berlin
Hoto: Reuters/F. Bensch

Ministan harkokin cikin gida na tarayyar Jamus Thomas de Maiziere ya ce mutum nan dan kasar Pakistan da aka kama bisa zarginsa da kai hari da babbar mota a kasuwar Kirsimeti da ke Berlin ya ce ba shi da hannu kan harin na daren jiya. To sai dai duk da wannan ikirari da mutumin ya yi, ma'aikatar cikin gidan Jamus din ta ce ta na cigaba da bincike kuma ta ce ya zuwa ynazu ba wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari da ya yi sanadin rasuwar mutane 12. Shi dai wannan mutum da ake zargi da kai harin ya fito ne daga Pakistan kuma ya shiga tarayyar Jamus a ranar 31 ga watan Disambar shekarar da ta gabata kana ya isa Berlin a watan Fabrairun bana.

Deutschland Angela Merkel, Thomas de Maziere und Frank-Walter Steinmeier am Breitscheidplatz
Merkel ta bi sahun Jamusawa wajen sanya fure a inda aka kai hari BerlinHoto: Reuters/H. Hanschke

A daura da wannan kuma, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai ziyara kasuwar Kirsimeti ta birnin Berlin da aka kai harin ranar Litinin. Bayan bayyana alhininta ga mutanen da suka rasu da iyalansu Angela Merkel ta ajiye furanni a daidai wurin da aka kaddamar da harin a kasuwar. Da ta ke jawabi a gaban manema labarai kafin ziyartar kasuwar kristiman ta birnin Berlin, Angela Merkel ta bayyana fatan ganin maharin bai kasance daga cikin jerin bakin da aka bai wa mafaka a kasar ba. Merkel ta kuma kara da cewa ala kulli halin wannan hari ba zai tsorata su ba, ba kuma zai sa Jamusawa su fasa gudanar da irin wadannan kasuwanni na Kristimati masu cike da tarihi ba, wadanda ke kasancewa matattarar iyalai a filin Allah ta'ala a duk karshen shekara.