Rashin matsugunai ga waɗanda yaƙi ya ɗaiɗaita | Siyasa | DW | 19.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rashin matsugunai ga waɗanda yaƙi ya ɗaiɗaita

A daidai lokacin da ake bikin ranar jinƙai na duniya, Somaliya ta samu ci -gaba da ma gwamnatin da al'ummar ƙasa da ƙasa ta amince da ita. Sai dai har yanzu akwai mutane dubu 300 da ba su da matsugunai na gari.

Tattalin arziƙin ƙasar Somaliya ya fara farfaɗowa, kuma har ƙasashe irin su Birtaniya da Turkiyya sun buɗe ofisoshin jakadancinsu a babban birnin ƙasar wato Mogadishu, inda al'ummar ta shafe shekaru da dama ta na fama da yaƙi da yunwa. Yau an yi shekara guda da samun sabon shugaban ƙasa Hassan Sheikh Mahmud wanda al'ummar ƙasa da ƙasa ta amince da shi. Sai dai kuma bunƙassar tattalin arziƙin ba ya tasiri yadda ya kamata domin akwai aƙalla mutane dubu 370 waɗanda suka rasa matsugunnensu kuma suna rayuwa cikin yanayin da bai dace a ce bil Adama na rayuwa a ciki ba.

A sansanin Darwish da ke tsakiyar birnin Mogadishu, ɗakuna ne suka gina da itatuwa suka rufe da ledoji da tsummokara, a nan mutane 400 ke amfani da bayi guda. Abinda ko a bisa tanadin dokokin ƙasa da ƙasa mutane 50 kaɗai ya kamata a ce sun yi amfani da bayi ɗaya. Wannan rashin kyautatuwar muhalli dai ya kasance wani sabon bala'i ga mutane dubu 300 da ke zama a wannan wuri. Nimo Mohammed Maahi ɗaya daga cikin wadanda ke zama wannan sansani ne tare da iyayenta da mai gidanta da 'ya'ya biyar

Fargabar masu zama a sansanoni

"Ina fargabar makomarmu yanzu, yara biyar gare ni, a cikinsu akwai 'yan uku waɗanda suka cika wata guda yanzu da haihuwa, a halin da muke ciki yanzu bamu hagen samun wata mafita, ban ma san yadda zamu yi ba, har a ce na ma tura yara na makaranta nan gaba, bamu ma da hanyar samun na ci bare na sanyawa, ina cikin damuwa ƙwarai"

'yan ukun da ta haifa na buƙatar abinci na musamman domin mahaifiyarsu ba ta da isashen ruwan nono, gaba ɗaya iyalin na dogaro da kuɗin da surukin na su kan samo kowace rana ne daga wajen ƙwadago, wuni mai kyau a wajensu shine su ci abinci sau biyu, wanda ya ƙunshi wake da masara da garin tuwo wata sa'a kuma haka nan suke zama. Ƙungiyar agaji ta Save the Children ce ta gina masu wajen kewayawar kuma ta kan basu ruwan sha da magunguna amma waɗannan ba su kaiwa koina a cewar Susan Collyer jami'a a ƙungiyar ta Save the Children:

Rawar ƙungiyoyin agaji wajen tallafawa 'yan Somaliya

"Wannan matsala ce da ke buƙatar matakan gaggawa ta kowani fanni musamman tamowa a ƙananan yara, to sai dai ana iya cewa an sami sauƙin matsalar idan aka kwatanta da abin da aka sani shekaru biyu da suka gabata lokacin da aka yi fama da yunwa mai tsanani, amma duk da haka akwai matsala kuma ƙorafin mafi yawan waɗanda ke zama wannan sansani shi ne sun fi samun tallafi shekara ɗaya da ya gabata da yanzu, a baya mun riƙa samun tallafi daga ƙungiyoyi daban-daban mun ma riƙa samun abinci daga al'ummar ƙasa da ƙasa wanda muka riƙa kaiwa waɗannan sansanonin amma mun daina yin haka yanzu saboda bamu samun tallafi"

A ko da yaushe waɗannan mutane ke buƙatar tallafi kuma kudin ba ya isa. haka nan kuma yanayin da sansanin ke ciki, bai dace a ce ɗan adam ya kasance cikin shi na wani tsawon lokaci ba. Waɗanda suka dawo daga gudun hijira suna neman zama a gidajensu amma kuma akwai waɗansu daban zaune wurin, amma kuma masu aikin agaji na ganin cewa waɗanda yaƙin ya ɗaiɗaitan suna buƙatar wani wuri ne na musamman, inda za a samar musu tsabtattacen ruwan sha, wurin kewayewa da kuma ofishin 'yan sanda, kuma wannan shirin ne kowa ya sanyawa gwamnatin ido ya gani ta aiwatar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin