Rashin kyaun yanayi ya adabi jihar California | Labarai | DW | 06.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rashin kyaun yanayi ya adabi jihar California

Mutane biyu sun rasu sakamakon matsanancin sanyin hunturu a jihar California ta ƙasar Amirka. Ruwan sama da iska mai ƙarfi sun halaka wata mata a birnin Los Angeles sannan wani ma´aikaci ya gamu da ajalinsa lokacin da wata bishiya ta faɗi akansa a birnin Sacramento. Tun a ranar juma´a da ta gabata mazauna a jihar ta California suke fama da iska mai karfi da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da kuma dusar kankara. Yanzu haka an samu katsewar wutar lantarki a gidaje dubu 600 yayin da mutane dubu hudu suka bar gidajensu don fargabar zazzayawar ƙasa. A kuma jihar Nevada dake makwabtaka wata ambaliyar ruwa ta sa a tilas an kwashe dubban mutane zuwa tudun mun tsira.