Rashin isassun kudaden yaki da yunwa a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 10.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rashin isassun kudaden yaki da yunwa a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba ta da kudin yaki da matsananciyar yunwa da ke barazana ga miliyoyin mutane a Sudan ta Kudu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kaso kadan take da shi na yawan kudaden da take bukata wajen yaki da barazanar matsalar yunwa a Sudan ta Kudu. Mai kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu Eugene Owusu ya ce ya zuwa yanzu kashi biyu cikin 100 na dala miliyan dubu 1.3 da suke bukata kawai suka samu. Mutane kimanin miliyan 2.8 a kasar wadda tun a karshen shekarar 2013 ta tsunduma cikin yakin basasa, ke bukatar taimakon abinci cikin gaggawa. Akalla mutane dubu 40 a cikinsu na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa. Jami'in ya ce ana bukatar tura kayan abinci cikin gaggawa zuwa yankunan kasar da tun faduwar damina a cikin watan Yuni ke da wahalar kaiwa saboda rashin hanyoyi masu kyau.