Rashin imanin ′yan sanda a Jamus | Zamantakewa | DW | 07.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rashin imanin 'yan sanda a Jamus

Kungiyoyin kare hakkin 'yan Adam suna zargin 'yan sandan Jamus da laifin wuce-gona-da iri da gallazawa jama'a.

A nan Jamus ko wace shekara a kan sami kararraki fiye da 2000, kan 'yan sanda da ake zargi da laifukan da suka hada har da amfani da karfi fiye da kima kan jama'a. Daga cikin wadannan kararraki, har da wanda wata mace ta gabatar, wanda a bayan da ta kira yan sanda saboda rikicin da ya tashi tsakaninta da mijinta, amma sai suka gwada mata karfi, wai saboda su kare kansu.

Shugaban rundunar yan sandan birnin Cologne, Udo Behrendes dake hira da tashar DW, ya ce a zahiri ba'a san yawan kararrakin dake kan yan sanda saboda rashin imanin su kan jama'a ba, saboda haka ne wannan matsala ba za'a taba shawo kanta gaba daya ba saboda ta kan aikinsu, yan sandan sukan wuce gona da iri lokaci-lokaci. Udo Behrendes dai mutum ne da ya kware kan aikinsa, domin kuwa ya shugabanci ofisoshin yan sanda akalla hudu a birnin na Cologne, ciki har da ofishin dake yankin nan mai matukar wahala na Eigelstein, inda aka taba zargin wani dan sanda da cin mutuncin wani mutum da har ya zama sanadin mutuwarsa. Behrendes yace bayan wannan hadari sai da shi da mataimakansa suka dauki shekara daya da rabi suna binciken abin da ya jawo haka, suka kuma yiwa tsarin aiyukan ofishin na yan sanda tankade da rairaya, inda a bayan haka, yan sandan suka sami wata sabuwar alkiba, suka kuma fahimci abinda aikinsu kan jama'a ke nufi. A takaice, yan sandan sun gane cewar a duk inda wani rikici ya tashi, ba karfinsu ake bukata ba, abin so shine su nuna gwanintar sulhu da daidaita juna. Hadin kai da aiki tare kuma ba yana nufin a boye kura-kuran abokan aiki bane idan sun yi.

Schleuserjagd an der Kabinentür

Binciken kan iyaka daga rundunar yan sandan Tarayya

To sai dai masani a kan aiyukan yan sanda, Thomas Feltes yana ganin irin wannan mataki na magance kura-kuran yan sanda a dangantakarsu da jama'a ba abu ne da aka saba samunsa yau da kullum a rundunonin yan sanda na kasar ta Jamus ba.

"Yace dangane da haka, akwai matsala ta tsarin aiki. Hakan kuwa yana tattare ne da gaskiyar cewar batun shawo kan matsalar kura-kurai a aikin yan sanda, musamman a wasu ofisosin yan sanda da ake dasu, kamary adda ake samun kura-kurai a dukkanin sauran fannoni na rayuwar yau da kullum, abune dake bukatar gyara matuka."

Symbolbild Polizeigewalt

Alamar rashin imanin yan sanda kan masu zanga-zanga

Sau tari shugabannin 'yan sanda suka kare ma'aikatansu, ba tare da sun san gaskiyar laifuka ko kura-kuran da yan sandan nasu suka aikata ba. Dalilin hakan shine, mafi yawan shugabannin yan sandan wannan zamani, sun sami horonsu ne shekaru 20 ko 30 da suka wuce. A wancan lokaci, akwai akidar dake cewar wai dan sanda baya aikata kuskure. A yau, inji Alexander Bosch na kungiyar kare hakkin yan Adam ta Amnesty International, batun kare hakkin jama,a shine kan gaba a aiyukan yan sanda, ko da shike akwai banbanci tsakanin horon da yan sandan suke samu a makarantu da kuma abinda sukan taras na yau da kullum idan suka kama aiki. Bosch yayi korafin cewar da zaran an gano wani laifi na yan sanda, nan da nan, ba tareda wnai bincike na kirki ba, akan rufe ala'amarin. Saboda haka ne ya gabatar da shawarar kirkiro wata hukumar bincike mai zaman kanta, kamar yadda ake dasu a wasu kasashe da zata rika binciken laifukan da ake zargin yan sanda da aikata kan jama'a. Sai dai ya zuwa yanzu, yan siyasa sun ki karbar wannan shawara, ko da shike majalisar dinkin duniya da kungiyar hadin kan Turai tuni suke baiyana bukatar amincewa da ita.

Mawallafi: Peßler/Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal