Rashin ci gaba a kokarin warware rikicin yan tawaye a Mali | Siyasa | DW | 11.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rashin ci gaba a kokarin warware rikicin yan tawaye a Mali

Faransa ta sanar da cewar zata goyi bayan bukatar Mali dake neman taimakon makamai a yunkurinta na kawo karshen aiyukan yan tawaye musulmi da suka mamaye arewacin kasar.

Faransa ta sanar da cewar zata goyi bayan bukatar kasar Mali game da samun taimakon makamai a yunkurinta na kawo karshen aiyukan yan tawaye musulmi da suka mamaye arewacin kasar. Shugaban kasa Francois Hollande shine ya baiyana haka, lokacin wani jawabi ranar Jumma'a a birnin Paris. Shugaban dake maida martani a game da rokon taimako da Mali tayi, yace Faransa zata duba wannan bukata, bisa dacewa da sharuddan da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya shimfida a watan Disamba na bara.

Rokon taimakon makamai da kasar ta Mali tayi, yazo ne a daidai lokacin da yan tawayen da suka mamaye arewacin kasar suke kara samun nasarori a kokarin su na kame wurare a kudancinta. Duk da haka, kuma duk da kudirin da majalisar dinkin duniya ta gabatar a karshen shekarar da ta wuce, amma kasashen Turai ya zuwa yanzu sun rufe kunnuwansu ga bukatun na Mali. Jaridar Faransa mai suna Le Figaro ranar Jumma'a ta rawaito cewar kasashen Turai suna iya baiwa Malin taimakona gaggawa. Tuni sojojin Faransa da na Jamus suka kakkafa sansanoninsu a garin Sevare a tsakiyar Mali, inda suke samun taimako da goyon baya a aiyukan su daga jiragen sama da motocin yaki. Jaridar ta kai ga tambayar shin ko tuni ma nahiyar Turai ta shiga yaki da yan tawayen ne na musulmi da suka fara sabon yunkuri da makamai daga arewacin kasar ta Mali kuma suke neman mamaye garin Sevare. Ma'aikatar tsaron Jamus ta musunta haka, inda ma tace babu sojan Jamus ko daya a Mali. Shima ministan harkokin waje, Guido Westerwelle ya tabbatar da wannan bayani, lokacin wani taro na menema labarai da ya kira.

Westerwelle Mali Ankunft Reise Flugzeug Tiéman Hubert Coulibaly

Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle a Mali

"Yace maida kokarin shawo kan rikicin kasar Mali ta hanyar amfani da karfin soja kadai ba zai yiwu ba. Saboda haka wajibni ne a kara kokarin neman warware wannan matsala ta amfanida hanyoyin siyasa. Tilas ne aci gaba da shawarwarin neman sulhu karkashin kungiyar kasashen Afirka."

Kungiyar hadin kan Turai tace taimakon da zata iya baiwa rundunar tsaron Mali a gwagwarmayar ta kan yan tawayen Mali ba zai wuce na horad da sojoji da kayan yaki ba. Shima wnanan taimako ba zai samu ba sai an cika wasu sharudda na musamman, in ji minista Westerwelle, inda yace:

"Daga cikin wadnanan sharudda har da samar da wani shiri mai karbuwa a game da sake maida kasar Mali karkashin tafarki na democradiya da tsarin mulki."

A daura da Westerwelle, shugaban Faransa, Francois Holand a jawabinsa ranar Jumma'a, ya nunar da shirinsa na bada gudummuwa a game da kawo karshen sabon yunkurin yan tawayen na Mali, amma bai yfadi yadda hakan zai samu ba, ko kuma Faransa zata shigar da sojojinta a wannan kokari, kuma yace Faransa ba zata yi gaban kanta a wnanan al'amari ba. Zata yi aiki ne bisa dacewa da kudirin kwamitin sulhu na na majalisar dinkin duniya. Tun a shekara ta 2012 kwamitin sulhun ya amincer da kudirin tura rundunar kasa da kasa zuwa Mali karkashin jagorancin nahiyar Afrika. Wolfran Lacher na cibiyar nazarin kimiya da siyasa a Berlin yace:

Soldat Militär Mali September 2012

Faratin rundunar tsaron Mali a Bamako

Babu tantama za'a samar da wannan runduna. To amma har yanzu ba'a shawo kan matsaloli da dama tattare da aiyukan da rundunar da za'a tura zuwa kasar Mali zata yi ba. Misali, za'a iya samar da wannan runduna cikin gaggawa? Wadanne kasashe ne zasu bada gudummuwar sojoji? Ina za'a sami kudaden tafiyar da aiyukan wannan runduna. Tilas ne kuma a lura da cewar babu mai wata masaniya game da halin da ake ciki a zahiri a ita kanta kasar ta Mali.

Wannan ma shi ya sanya Wolfram Lacher yake baiyana shakkar ko rundunar da za'a tura kasar Mali zata samu cikin gaggawa nan gaba kadan tare da taimakon kasashen Turai. Sabon yakin da yan tawayen na Mali suka tayar a kwanan nan kuma, ba zai taimakawa gwamnatoci a Berlin da Paris su yanke kudiri cikin gaggawa ba.

Mawallafi: Peter Hille/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin