1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Ziyarar karfafa cinikayya da Afirka

Ramatu Garba Baba
March 8, 2018

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fara ziyarar kwanaki biyar a wasu kasashen Afirka, makasudun rangadin shi ne karfafa hadin kai musamman a fannin tattalin arziki da ciniki a tsakanin Rashar da Afirka.

https://p.dw.com/p/2txQ2
Namibia | russischer Außenminister Sergei Lawrow mit Namibias Präsident Hage Geingob
Hoto: imago/ITAR-TASS/A. Shcherbak

A wannan makon ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fara ziyarar kwanaki biyar a wasu kasashen Afirka da suka hada da Angola da Namibiya da Mozambik da Zimbabuwe da kuma Habasha wato Ethiopia. Lavrov ya fara yada zango ne a kasar Angola inda ya tattauna da shugaban kasar Joao Lourenco da kuma takwaran aikinsa na Angola Manuel Domingos Augusto a kan dadaddiyar huldar danganta a tsakanin kasashen biyu. Lavrov ya nuna bukatar inganta samun hadin kai a fannonin ilimi da makamashi da kuma na soji.

Angola | russischer Außenminister Lawrow besucht Gedenkstätte
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei LavrovHoto: imago/ITAR-TASS/A. Shcherbak

Baya ga Angola Lavrov na kuma ziyararta kasashen Namibiya da Mozambik da Zimbabuwe da kuma Habasha. Saboda haka ne Yevgeniy Korendyasov da ke zama tsohon jami'in diplomasiyyar tshouwar Tarayyar Sobiet a kasar Burkina Faso kuma daga baya ya zama wakilin Rasha a Mali amma yanzu ya ke jagorantar cibiyar nazarin huldar dangantaka a tsakanin Rasha da Afirka a birnin Mosko ya ce ziyarar ministan na da burin farfado da tsohuwar dangantakar Rasha da kawayenta na Afirka.

Rasha na da muradin fadada huldodin ciniki da tattalin arziki da Afirka, inda kuwa albarkatun karkashin kasa ke taka muhimmiyar rawa. Rasha na matukar bukatar danyun kaya daga ketare kasancewa wanda take da shi a cikin gida ko kadan ba su kai abin da take bukata ba. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da Lavrov ya zabi kasashen hudu na Afirka yake kai wa ziyara. A Namibiya ga misali na kan hanyar zama kasa ta uku mafi hako karfen uranium a duniya, a Mozambik wani kamfanin Rasha Rosneft ke aikin hakar man fetir.

UN Sicherheitsrat Abstimmung über Waffenruhe in Syrien
Lavrov ya nuna goyon baya na bai wa kungiyar AU kujerar dindindin a Kwamitin Sulhu na MDDHoto: Getty Images/AFP/D. Emmert

A tattaunawa da ya yi a Namibiya a ranar Talata, Lavrov ya nuna goyon baya ga kungiyar tarayyar Afirka kana ya yi kira da a ba wa Afirka kujerar dindindin a Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya. A Habasha inda ake bikin cika shekaru 120 da kulla dangantaka tsakanin kasar da Rasha, ana dab da kammala shirye-shiryen zirga-zirgar jirgin sama kai tsaye tsakanin kasashen biyu. Sai dai kuma Yevgeniy Korendyasov da jagoran cibiyar nazarin huldar dangantaku tsakanin Rasha da Afirka a birnin Mosko ya ce bangarorin biyu na musayar yawu a kan yaki da ta'addanci da kuma matsalar yunwa a Afirka.