Rasha zata nunawa Hamas damuwar kasashen duniya | Labarai | DW | 11.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha zata nunawa Hamas damuwar kasashen duniya

Rasha ta tabbatarwa gamaiyar kasa da kasa cewa zata aike da wani sako ga kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas don ta yi watsi da tashe tashen hankula. A halin da ake ciki sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta tattauna da takwaranta na Rasha Sergei Lavrov ta wayar tarho, bayan matakin ba zata da gwamnati a birnin Mosko ta dauka na gayyatar kungiyar Hamas, wadda ta lashe zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinawa. Isra´ila, wadda ke son manyan daulolin duniya su juyawa Hamas baya har sai ta amince da ´yancin wanzuwar kasar Bani Yahudu kana kuma ta ajiye makamai, ta nuna adawa da wannan gayyata. KTT da kuma Amirka na daukar Hamas a matsayin wata kungiya ta ´yan ta´adda saboda haka sun ce ba zasu yi wata hulda da ita ba a cikin lokacin nan da ake ciki.