Rasha za ta tsaigaita wuta a Aleppo | Labarai | DW | 20.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha za ta tsaigaita wuta a Aleppo

Kasar Rasha ta amince da cimma yarjejeniar tsagaita bude wuta da take yi a gabashin birnin Aleppo da zai bawa kungiyoyin agaji damar kai doki ga fararen hula.

Majalisar Dinkin Duniya na yunkurin ganin ta ja hankalin kasar Rasha na ganin ta tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar daga kwanaki uku zuwa hudu. Ana sa ran wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta da Rasha ta cimma zai fara aiki nan ba da jimawa ba, don bawa kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya ta Red Cross damar kai doki ga daruruwan marasa lafiya da wadanda suka jikata a yayin gumurzun wuta tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan kasashen waje.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta gargadi dukkannin bangarorin da ke gwabza fada a yankin na Aleppo da su mutunta yarjejeniyar da zai baiwa jami'an agaji shiga yankunan da fararen hula ke ciki.