Rasha za ta sasanta Amirka da Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 26.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha za ta sasanta Amirka da Koriya ta Arewa

Bayan tsamin dangantakar da ke tsakanin Shugaba Kim Jong-Un da Donald Trump, kasar Rasha na fatan shiga tsakanin bangarorin biyu da nufin kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu.

Gwamnatin kasar Rasha ta sanar cewa tana yunkurin sulhunta tsamin dangantakar da ke tsakanin kasashen Amirka da Koriya ta Arewa, in har bangarorin biyu sun amince da wannan tayin.

Ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ya yi kira ga kasashen biyu da su hau teburin sulhu bayan kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kakaba wa kasar ta Koriya ta Arewa takunkumi a makon da ya gabata, sakamakon gwajin makaman kare dangi da kasar ke ci gaba da yi wanda ke zama barazana ga duniya baki daya.