Rasha za ta janye sojoji daga Siriya | Labarai | DW | 11.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha za ta janye sojoji daga Siriya

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayar da umurnin kwashe mafiyawancin sojojin kasarsa da ke a kasar Siriya inda ya kai wata ziyarar ba za ta a barikin sojoji na Hmeimin inda sojojin Rashar ke girke.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayar da umurnin kwashe mafiyawancin sojojin kasarsa da ke a kasar Siriya zuwa gida. Ya sanar da hakan ne a lokacin wata ziyarar ba zata da ya kai a wannan Litinin a cibiyar sojoji ta Hmeimin inda sojojin Rashar ke girke. 

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Rasha na Interfax ya ruwaito Shugaba Putin din na cewa a tsawon shekaru biyu da suka gabata sojojin Rashar tare da takwarorinsu an Siriya sun yi nasarar karya lagon kungiyoyin 'yan ta'adda, a dan haka ne a yanzu ya dauki wannan mataki na mayar da akasarin sojojin Rashar zuwa gida. 

Shugaban kasar ta Siriya Bashar al-Assad da ministan tsaron kasar Rasha Serguei Choigou da babban kwamandan sojojin Rasha a Siriya Janar Serguei Sourovikine ne suka tarbi Shugaba Putin a ziyarar ba zatar da ya kai a barikin sojojin ta Hmeimin.