1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha za ta gina wa Masar tashar nukiliya

Gazali Abdou Tasawa
December 11, 2017

Kasashen Rasha da Masar sun cimma yarjejeniyar gina wa kasar ta Masar tashar makamashin nukiliyata ta farko da za ta samar da megawatt dubu biyar na makamashi ga kasar.

https://p.dw.com/p/2pAtt
Putin und Al-Sisi in Sotschi 12.08.2014
Hoto: dpa/Alexey Druginyn/RIA Novosti/Kremlin

Kasashen Rasha da Masar sun cimma yarjejeniyar gina wa kasar ta Masar tashar makamashin nukiliyata ta farko. Shugabannin kasashen biyu wato Abdel Fattah al-Sissi da Vladmir Putin ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya a wannan Litinin a birnin Alkahira inda shugaban kasar ta Rasha ya isa a ci gaban rangadin da yake gudanarwa a wasu kasashen duniya. 

Yarjejeniyar ta tanadi gina tashoshin guda hudu a yankin Dabaa inda ko wace za ta samar da megawatt dubu da 200 na makamashi. Kudi biliyan 30 na dalar Amirka ne shirin zai lakume.

Bayan ganawarsa shugabannin biyu inda suka tattauna batun rikicin Isra'ila da Palasdinu, Shugaba Putin ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kira go komawa kan tebirin tattaunawa tsakanin Isra'ila da Palasdinun musamman kan batun birnin Kudus wanda Amirka ta ayyana a baya bayan nan a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.